Shahararriyar Mawakiya Tiwa Savage Ta Fadi Wanda Ya Fitar da Bidiyon Tsiraicinta
- Tiwa Savage ta bude babin da aka yi kokarin rufe tun 2021 lokacin da aka ga bidiyon tsiracinta yana yawo a Intanet
- A wata tattaunawa da aka yi da ita, tauraruwar ta Afrobeats ta bayyana cewa tsohon saurayinta ne ya ci amanarta
- Savage ta ce tsohon saurayin nata ya wallafa bidiyon a intanet da gangan domin ya ci caca da suka yi da abokinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Fitacciyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage ta yi magana game da halin da ta shiga da aka yada wani bidiyon ta.
A kwanakin baya bidiyon tsiracin mawakiyar mai shekaru 46 a duniya ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani.

Source: Getty Images
Tiwa Savage ta tuno abin da aka yi mata
A wata hira da aka yi da ita, Leadership ta rahoto Tiwa Savage ta na bayanin yadda aka yi wannan bidiyo ya shiga duniya.

Kara karanta wannan
Umahi: A karshe ministan Tinubu da aka tsinci gawar budurwa a gidansa ya fadi abin da ya faru
Maganar da ta yi, ta tabbatar da sahihancin wannan bidiyo inda aka ce an ga ta tana mu’amala kwance tare da wani namiji.
Duk da abin ya yi mata ciwo, babbar tauraruwar ta bayyana cewa wani tsohon saurayin ta ne ya yi mata wannan danyen aiki.
Tiwa Savage ta ce tsohon saurayin ya fitar da bidiyon ne saboda ya ci caca da ya yi da abokinsa, amma ba ta kama sunayensu ba.
“Na yarda da shi a lokacin domin abokina ne, amma ban san cewa ya yi hakan ne saboda ya yi caca da wani abokinsa ba.”
Zancen Tiwa Savage ya jawo muhawara
Wannan magana tata ta sake bude bakin babin da aka yi kokarin rufe wa tun tuni a intanet.
Wasu masoya sun fito suna kare mawakiyar, suna cewa an ci amanar ta, wasu kuma sun yi mata kaca-kaca ganin har yaro ta haifa.
An fitar da wannan bidiyo ne ba ta amincewarta ba, wannan ya nuna matsalar da ake samu wajen nadar faifan tsiraci irin wannan.

Source: Getty Images
Saboda haka ne dai aka fara kira ga Gwamnatin Najeriya ta tsaurara doka ta yadda za a iya hukunta masu yin wannan mugun aiki.

Kara karanta wannan
Akpabio ya yi wa Oshiomhole shagube kan 'bidiyonsa' yana yi wa budurwa tausa a jirgi
Wadanda suka soki wannan cin amana sun ce ya kamata a wayar da kan maza da mata game da rike siri lokacin da ake soyayya.
James Iyanuoluwa Adio ya yi koyi da Tiwa Savage
Irin haka ta faru da wani dalibi a jami’ar FUOYE kwanan nan, aka dauka kuma aka saki bidiyon shi yana mu’amalar namiji da mace.
Kwanakin baya aka ga bidiyon tsiracin James Iyanuoluwa Adio wanda shi ne shugaban daliban jami’ar tarayya ta Oye Ekiti a jihar Ekiti.
Da aka yi hira da shi, Kwamred James Iyanuoluwa Adio ya yi bayanin yadda ya samu kwarin guiwa daga magabaciyarsa Tiwa Savage.
Ganin yadda mawakiyar ba ta bari abin ya taba rayuwarta ba a 2021, shi ma shugaban kungiyar ta SUG ya yi koyi da abin ya faru da shi.
An kai Tiwa Savage da Don Jazzy kotu
A shekarun baya an taba ji Danny Young (Olumuyiwa Danladi) ya kai karar mawakiya Tiwa Savage tare da Don Jazzy a Kotun tarayya.
Danny Young na zargin Savage da yin amfani da basirarsa ta hanyar satar baitoci ko salon wakarsa a cikin wakar ta ba tare da ya ba ta izini ba.
An hada mawakiyar da shugaban kamfanin Mavin Records za a yi shari'a da su a shekarar 2019, ana neman su biya makudan miliyoyi.
Asali: Legit.ng