Danny Young ya kai Tiwa Savage da Don Jazzy kara a Kotun Tarayya

Danny Young ya kai Tiwa Savage da Don Jazzy kara a Kotun Tarayya

Babban kotun tarayya da ke zama a Legas ya sa Ranar 5 ga Watan Nuwamban gobe a matsayin ranar da za a saurari karar da a ka kai Taurarauwar Mawakiyar nan Tiwatope Savage.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto a yau 24 ga Watan Oktoba, 2019, Olumuyiwa Danladi wanda aka fi sani da Danny Young shi ne ya kai karar wannan Mawakiya gaban Alkalin babban kotu.

Danny Young ya na neman Alkali mai shari’a Mohammed Liman na babban kotun tarayyar ya sa Tiwa Savage kamar yadda aka fi saninta, ta biya shi wasu kudi har Naira miliyan 205.

Mai karar ya na ikirarin cewa Tiwa Savage ta yi amfani da basirarsa wajen rera wata waka da ta sanyawa suna ‘ONE’. Danny Young yace an ci da guminsa ba tare da ya bada izni ba.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari zai hukunta Malamai masu lalata da ‘Dalibai

Mai tuhumar ya kuma maka kamfanin Marvin Records a wannan kara. Don Jazzy wanda ya yi fice a fadin Nahiyar Afrika shi ne ya kafa wannan kamfani shekaru bakwai da su ka wuce.

Mawakin da ya yi tashe da wakarsa ‘Omo Lepa’ ya na bukatar a biya shi fiye da Naira miliyan 200 ne da nufin ya rage zafi a kan satar basirarsa da aka yi wajen rera wata wakar da ya yi.

Lauyan Mawakin ya kuma bukaci karin Naira miliyan biyar daga hannun Mawakiyar. Har ila yau, wannan Mawaki ya nemi kotu ta ba shi duk ribar da aka samu daga wakar ta “ONE.”

Justin Ige shi ne Lauyan mai kara a shari’ar da aka sa za a yi a Ranar 5 ga Wata. Tun farkon shekarar nan Danny Young ya shigar da kara amma wanda ake zargi sun ki cewa komai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel