Dalilin da yasa bana son kallon bidiyon jima'i na Tiwa Savage, Shehu Sani

Dalilin da yasa bana son kallon bidiyon jima'i na Tiwa Savage, Shehu Sani

  • Tsohon ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, yace baya son kallon bidiyon Tiwa Savage
  • Sanata Sani ya gargaɗi mutane da kada wanda ya turo masa domin idan ya kalla zai iya faɗuwa ya sume
  • A cewarsa karo na karshe da ya kalli makamancin irin wannan bidiyon sai da ya kwashe awanni 24 a gadon Asibiti

Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa baya son kallon bidiyon jima'i na Tiwa Savage, dake yawo a kafafen sada zumunta.

Tsohon sanatan kuma mamba a babbar jam'iyyar hamayya PDP, yace baya son kallon bidiyon ne saboda zai iya yanke jiki ya faɗi sumamme.

Sanata Shehu Sani
Dalilin da yasa bana son kallon bidiyon jima'i na Tiwa Savage, Shehu Sani
Asali: UGC

Sanata Shehu Sani ya faɗi haka ne a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook, jim kaɗan bayan sakin bidiyon, kuma ya karaɗe kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

Meyasa Sanata Sani zai faɗi daga kallon bidiyo?

Sani ya ƙara da cewa a baya da ya kalli bidiyo makamancin irin wannan na jima'i, yanke jiki ya yi ya faɗi sumamme sabida kaɗuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatan yace:

"Gargaɗi: Dan Allah kada wanda ya turo mun bidiyon Tiwa Savage, domin kada a samu matsala na sume."
"Karo na ƙarshe da na kalli makamancin irin wannan bayan wani ya turo mun, ban san abinda ya turo ba, sai da na kwanta a gadon asibiti na kwana ɗaya."

A wani labarin na daban kuma Sabbin zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau a wurin daukar fim a Bollywood Indiya sun sake bayyana

Tun a baya dai Sadau ta buga hotuna a dandalinta na sada zumunta, inda tace tana aikin shirin fim da masana'antar Bollywood.

Rahama Sadau, ta saba jawo cece kuce kan shigar da bata dace da addininta ba kuma ta dora a kafar sada zumunta.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje

Asali: Legit.ng

Online view pixel