An Yi Wa Shahararriyar Mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage, Fashi a Landan

An Yi Wa Shahararriyar Mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage, Fashi a Landan

  • Shahararriyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage ta labartawa mabiyanta yadda ta gamu da 'yan kwanta-kwanta birnin Landan
  • Mawakiyar ta bayyana cewa wasu bata gari sun yi mata fashi da tsakar rana a Landan, inda ta ɗora hoton ta tsaye a wajen
  • Duk da sanar da hakan, Savage ba ta yi wani karin bayani kan kayayyaki ko kudin da aka sace mata ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rahotanni sun bayyana cewa shahararriyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage ta gamu da 'yan kwanta-kwanta a birnin Landan, sun yi mata fashi da makami.

Mawakiyar ta tabbatar da wannan mummunan lamari da ya faru da ita a shafin ta na Instagram, a ranar 18 ga watan Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Bincike ya gano jihohin Najeriya 10 da aka fi samun man fetur da araha

An yi wa Tiwa Savage fashi a Landan.
An yi wa mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage fashi da rana a Landan, ta bada labari. Hoto: @tiwasavage
Asali: Instagram

Nawa aka sacewa mawakiyar?

Da take nuna hotonta tsaye a wajen, Tiwa Savage ta wallafa cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Haba dai Landan, lallai na gamu da 'yan iya shege, sun yi mun fashi jiya."

Duk da cewa mawakiyar Koroba ba ta sanar da adadin kudin da aka kwace mata ba, sai dai ta nuna damuwarta kan hakan.

Har zuwa haɗa wannan rahoton Legit Hausa ba ta sani ba ko an kama barayin ko akasin hakan.

Kalli abin da ta wallafa a nan kasa:

Tiwa Savage a Landan
An yi shahararriyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage, fashi a Landan. Hoto: @tiwasavage
Asali: Instagram

An taba yi wa Makinwa fashi a Landan

Ba wai mawakiya Tiwa Savage ce kadai shahararriya 'yar Najeriya da aka taba yi wa fashi a birnin Landan ba.

Ko a shekarar 2022 sai da aka yi wa shahararriyar mai gabatar da shirye-shirye a TV, Toke Makinwa fashi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutumin da ya kitsa garkuwa da kansa don damfarar yan uwansa a Abuja

Makinwa ta ce barayin sun yi awon gaba da kudade da wasu kayayyakin ta masu muhimmanci.

Tiwa Savage ta fara fitowa a fina-finai

A wani labarin kuma, Legit.ng ta ruwaito maku cewa mawakiya Tiwa Savage ta sanar da cewa ta fara fitowa a fina-finai, kuma ta fara fim din ta na farko mai suna 'Water and Garri'.

A cewar Tiwa a shafinta na Instagram, wacce ke da gidan haya a birnin Landan, ta ce an kwashe shekaru biyu ana daukar shirin.

Ta kara da cewa shirin fim din na daga cikin manyan abubuwan da ta saka a gaban ta da take fatan samun nasara.

Ango ya mutu ana saura kwana uku daurin aurensa

A wani labarin na daban, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wani matashi mai suna Abraham Basif ya mutu a asibiti ana saura kwana uku daurin aurensa.

Mutuwar Basif ta jefa mutane cikin tashin hankali musamman ma wacce zai aure mai suna Praise Enyojo, wacce ta kusa zaucewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel