Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya yi magana kan batun satar akwatin zabe da magudi gabanin 2027.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya yi magana kan batun satar akwatin zabe da magudi gabanin 2027.
Fitaccen malamin addinin Musulmi, Sheikh Mansur Isah Yelwa ya dawo limanci a masallacin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi bayan kwana 4 da murabus.
A jiya Juma'a ne Alkalin Kotun Daukaka Kara ya dakatar da aiwatar da hukuncin da ya tabbatar da dawowar Sanusi II a matsayin Sarki inda kowa ke sha'aninsa a Kano.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana kudaden fansan da 'yan bindiga suka nema kan matashin mahaddacin Al-Kur'anin da suka sace a kwanakin baya a jihar.
Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Ahmad Aliyu ta shirya karya farashin kayan abinci. Gwamnatin ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa dakarun tsaro sun ƙara ƙaimi wajen farautar shugaban ƴan bindiga Kachalla Dan Mai Kinni, bayan cafke yaronsa, Lawali Malangaro.
Gwamnan jihar Nasarawa ya tara almajirai ya raba musu sadaka bayan sallar jumu'a. Gwamna Abdullahi Sule ya ce ya raba kudin ne saboda falalar azumi da neman lada.
Hukumar kashe gobara ta Kano ta bayyana cewa ta ceci mutane 7, yayin da gobara ta kashe 7 tare da haddasa hasarar dukiyar Naira miliyan 50 a watan Fabrairu.
Dakarun rundunar dojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 74 ta%e da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a samame daban-daban a makon jiya.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasarar dakile wani harin ta'addanci da 'yan bindiga suka yi kokarin kai wa a jihar Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Sojojin 'Operation Fansan Yanma' sun kashe 'yan ta'adda 12 a kauyen Maigora, Faskari, suka kwato babura da dama daga hannunsu.
Labarai
Samu kari