"Ka Daina Bayyana Kanka a Matsayin Sarkin Kano," Ɗan'agundi Ya Yi Wa Sanusi II Barazana

"Ka Daina Bayyana Kanka a Matsayin Sarkin Kano," Ɗan'agundi Ya Yi Wa Sanusi II Barazana

  • Rikicin sarautar Kano na ƙara tsanani tun bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara mai zama a babban birnin tarayya Abuja
  • Kotun ta umarci kowane ɓangare na shari'ar ya koma matsayinsa na usuli, matakin da tsagin Aminu Ado Bayero ke ganin sun yi nasara
  • Aminu Babba Ɗan'agundi ya yi barazanar kai karar Muhammadu Sanusi na II idan ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin sarkin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Aminu Babba Dan'agundi ya yi barazanar daukar matakin shari'a kan sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II idan ya ci gaba da zama a kan sarauta.

Ɗan'agundi wanda ke fafutukar kare Aminu Ado Bayero a shari'ar sarautar Kano, ya ce za su koma kotu idan Sanusi II ya ci gaba da kiran kansa a matsayin sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Madalla da hutu ga yan sakandare domin azumin watan Ramadan

Aminu Babba Dan'agundi da Sanusi II.
Dan'agundi ya yi barazanar sake maka Muhammadu Sanusi II a gaban kotu Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Ya ce hakan tamkar raina kotu ne bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta yanke, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan'agundi, wanda shi ne sarkin Dawaki Babba na masarautar Kano a lokacin Aminu Ado Bayero ya faɗi haka ne a wata hira da manema labarai a Kano.

Hukuncin kotu ya sauke Sanusi II?

Ya jaddada cewa hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, ya umarci dukkan bangarorin da su ci gaba da kasancewa a matsayin da suke kafin fara rikicin shari'ar.

Babba Ɗan'agundi ya ce:

"Abubuwa biyu muka roƙa a shari'ar. Na farko, neman umarnin wannan kotun mai daraja na dakatar masu daukaka kara da sauran wadanda ake kara daga aiwatar da hukuncin ranar 10 ga Janairu har sai kotun koli ta yi hukunci.
"Na biyu, mun roki kotu mai daraja ta bayar da umarnin ci gaba da kasancewa a matsayin da ake kafin fara shari'ar, kamar yadda aka kasance kafin hukuncin Mai Shari'a A. M. Liman (yanzu JCA) har sai kotun ƙoli ta raba gardama."

Kara karanta wannan

Sanusi vs Aminu Ado: An gargadi Abba Kabir da sauran hukumomi bayan hukuncin kotu

Kotu ta amince da buƙatar tsagin Aminu Ado?

Dan'agundi ya bayyana cewa kotun daukaka kara ta amince da dukkanin rokon da suka gabatar a hukuncin da ta yanke kwanan nan.

Ya ce muhimmin sashi na hukuncin shi ne umarni na biyu, wanda kotu ta umarci ci gaba da kasancewa a matsayin da ake kafin fara shari'ar, ma'ana masarautar dole ne ta koma matsayin da take na usuli.

"Abin da wannan ke nufi shi ne mu koma matsayin da muke kafin na kai kara don kalubalantar soke dokar masarautar Kano, wacce gwamnatin jiha ta yi amfani da ita wajen sauke dukkanin sarakunan.
"Wane matsayi muke a wancan lokaci? Shi ne Alhaji Aminu Ado Bayero ne sarkin Kano, sannan kuma muna da sarakuna guda huɗu," in ji shi.
Aminu Ado Bayero.
Dan'agundi ya yi barazanar maka Muhammadu Sanusi II a kotu Hoto: @HRHBayero
Asali: UGC

Ɗan'agundi ya yu wa Sanusi II barazana

Aminu Babba Ɗan'agundi ya gargadi cewa zai dauki matakin shari'a idan Sanusi II ya ci gaba da ikirarin zama Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

"Don haka idan saboda wani dalili, Sanusi ya bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, hakan zai zama raina kotu saboda wannan hukuncin.
"Ya kamata mu girmama dokar kasa, kuma idan saboda wani dalili, ya yanke shawarar yin akasin haka, zan kai shi kotu kuma in tuhume shi da raina kotu."

- In ji Ɗan'agundi.

Abin da gwamnatin Kano ta ce kan hukuncin

A baya, kun ji cewa gwamnatin Ƙano karƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta musanta rahoton cewa hukuncin kotun ɗaukaka kara ya soko dawo da Sanusi II.

Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Haruna Isa Dederi ya ce hukuncin da kotun ta yi a ranar 10 ga Janairu ya tabbatar da ikon gwamnati na dawo da Sanusi kan sarauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262