'Yan bindiga sun kashe Kanal Abdussalam Ude a birnin Abuja, yayin da matarsa, direbansa da jami'in tsaronsa suka jikkata. Ana ci gaba da bincike.
'Yan bindiga sun kashe Kanal Abdussalam Ude a birnin Abuja, yayin da matarsa, direbansa da jami'in tsaronsa suka jikkata. Ana ci gaba da bincike.
Wata kotun shari'ar musulunci ta zartar da hukunci kan wanu barawon babur da aka gurfanar da shi a gabanta a jihar Kano. Kotun ta tura shi zuwa gidan gyaran hali.
Rundunar yan sandan jihar Kwara ta bayyana cewa jami'an tsaron haɗin guiwa sun yi nasarar kama mutum 3 da ake zargi da hannu a sace basarake da wasu uku.
Kungiyar Miyetti Allah ta kaddamar da kungiyar 'yan sa kai don yakar 'yan bindiga da barayin shanu a jihar Nasarawa. Kungiyar ta horas da fulani 1,114 don yin aikin.
Bayan tuntuba da dama, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Ayodele, ya bayyana cewa zai gina masallacin na miliyoyin naira a Legas.
'Yan bindiga sun kashe wani magidanci mai suna Tijani Amedu tare da yin garkuwa da kananan yara 13 a hanyar Kaduna, kuma sun nemi kudin fansa naira miliyan 60.
A ranar 14 ga watan Janairu, 2024 kamfanin 'Retail Supermarket Nigeria Limited (RNSL) ya sanar da rufe kantin Shoprite na Kano, tare da fadi dalilin daukar matakin.
Gwamnatin tarayya ta sake shigar da sababbin tuhume-tuhume a shari'ar da take yi da tsohon gwamnan babban bankin Najeriiya (CBN), Godwin Emefiele.
Sarakuna daga kananan hukumomi uku sun tube Sanata Ifeanyi Ubah daga sarautar da suka nada shi yayin da Gwamnan jihar, Charles Soludo ya yaba musu.
Jarumar fina-finan Nollywood, Uche Ogbodo ta yi martani ga mazan da ke aika mata sakonni suna neman soyayyarta. Ta ce an la’anci matar aure da ke yawon bin maza.
Labarai
Samu kari