Rundunar Yan Sanda Ta Dauki Kasurgumin Dan Ta’adda, Bello Turji Aiki? ACP Adejobi Ya Fayyace Gaskiya

Rundunar Yan Sanda Ta Dauki Kasurgumin Dan Ta’adda, Bello Turji Aiki? ACP Adejobi Ya Fayyace Gaskiya

  • Rundunar yan sandar Najeriya ta yi gargadin cewa kasurgumin dan ta'adda da ake nema ido rufe, Bello Turji, ba jami'in tsaro bane duk da akwai hotunansa sanye da kayan yan sanda
  • Turji ya kasance daya daga cikin yan bindiga mafi hatsari a yankin arewa maso yammacin Najeriya tare da daruruwan mayaka a karkashin ikonsa
  • Kakakin rundunar yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce sabanin ikirarin da ke yawo a wasu bangarori, ba'a taba daukar Turji aiki a hukumar tsaron ba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana hasashen cewa an taba daukar kasurgumin dan bindiga, Bello Turji aikin dan sanda a matsayin kanzon kurege.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

ACP Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar yan sandan ne ya karyata zancen a ranar Laraba, 17 ga watan Janairu.

Rundunar yan sanda ta ce bata taba daukar Turji aiki ba
Rundunar Yan Sanda Ta Dauki Kasurgumin Dan Ta’adda, Bello Turji Aiki? ACP Adejobi Ya Fayyace Gaskiya Hoto: @ElochukwuOhagi, @PoliceNG
Asali: Twitter

Adejobi ya ce hoton Turji sanye da kayan yan sanda da ke yawo a yanar gizo "ba sabo bane".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya):

"Ba a taba daukar Turji aiki a rundunar yan sanda ba. Wannan hoton ba sabo bane."

Sojoji sun karyata batun kwace motoci masu sulke

A gefe guda, rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ake cewa shugaban ‘yan bindiga Bello Turji ya kama daya daga cikin motocinsu masu sulke.

Rundunar ta mayar da martanin ne bayan wani faifan bidiyo na yawo a kafafen sadarwa cewa dan bindigan ya samu nasarar kama motar yaki na rundunar, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Matashi ya gurfana a kotu kan zargin taba muhibbar malamin addini a Kano

An kashe yan bindiga a Benue

A wani labarin kuma, mun ji cewa jami'an tsaro a safiyar Laraba, 17 ga watan Janairu, sun hallaka wasu yan bindiga, yayin da suke kokarin dakile harin da suka yi yunkurin kaiwa al'ummar kauyen Tse Gaagum.

An dai yi musayar wuta mai zafi tsakanin jami'an tsaron da yan bindigar a kauyen Tse Gaagum dake gudunmar Ukemberegya, a karamar hukumar Logo dake jihar Benue.

Wasu da abun ya faru a idonsu sun shaidawa manema labarai cewa, jami'an tsaron sun fatattaki yan bindigar bayan fakar su da suka yi sakamakon kiran gaggawa da suka samu daga mazauna kauyen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel