Fasto Ya Umurci Mabiyansa Su Bashi Dukkan Albashinsu Na Watan Janairu, Ya Bayyana Fa’idar Hakan

Fasto Ya Umurci Mabiyansa Su Bashi Dukkan Albashinsu Na Watan Janairu, Ya Bayyana Fa’idar Hakan

  • Wani limamin coci, Fasto Anosike ya nemi mabiya cocinsa da su ba shi dukkan albashin su na watan Janairu don neman albarka a 2024
  • Ya ce ma damar mabiyansa sun dauke shi a matsayin ubansu na ruhaniyya, to su ba shi dukkan albashin su ba tare da gardama ba
  • Haka zalika ya ce shi ba ya tsoron gutsiri tsoma ko sukar jama'a, kuma zai mayar masu da kudinsu idan ba su samu albarka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wani limamin coci, Fasto Anosike ya shaida wa mabiya cocinsa cewa albashin da za su dauka na watan Janairu na shi ne ba na coci ba.

Faston ya yi ikirarin cewa ba ya tsoron gutsiri tsoma da sukar mutane, yana mai jaddada cewa albashin su na farko a 2024 nasa ne kawai, don amfanin kansa.

Kara karanta wannan

Kotu ta fara yanke hukunci kan shari'ar BBC da wani mawakin Kano

Fasto ya nemi mabiyansa su bashi duka albashin su na watan Janairu
Akwai fa'ida: Fasto ya nemi mabiyansa su bashi duka albashin su na watan Janairu. Hoto: @PstJohnAnosike
Asali: Twitter

Limamin cocin ya kafa sharadin mayar da kudin kowa

Ya ce ma damar mabiyansa sun dauke shi a matsayin ubansu na ruhaniyya, to su ba shi dukkan albashin su na Janairun shekarar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta ruwaito limamin cocin yana cewa irin wannan karramawar da za su yi masa ce za ta kawo musu albarka a 2024.

A cikin wani faifan bidiyo, faston ya yi ikirarin mayar masu da kudadensu idan har mambobin nasa ba su samu albarkar rayuwa ba nan da tsakiyar shekara.

Kalli bidiyon jawabin malamin addinin a nan:

Kadan daga abin da limamin cocin ya ce

"Idan kun bani kudin, zan yi amfani da su ga bukatar kaina, kuma zuwa tsakiyar wannan shekara, idan ba ku samu albarkar rayuwa ba, ku dawo, zan mayar muku da kudin ku.

Kara karanta wannan

Ayi Hakuri: Dalilin neman afuwar ‘Yan Najeriya kan wahalar da na Jefa su – Buhari

“Za ku ga abubuwan al'ajabi, nayi maku alkawari da ruhina, kuma Bulus ma ya ce, duk da ba na tare da ku, amma ina cikin ruhin kowannen ku."

Yan bindiga sun kashe magidanci, sun sace yara 13 a hanyar Kaduna

A wani labarin, 'yan bindiga sun tare hanyar Kaduna inda suka kashe wani magidanci mai suna Tijani Amedu ta hanyar bugun kansa, kuma sun yi awon gaba da kananan yara 13.

An ruwaito cewa Amedu da 'yan uwansa na kan hanyar komawa Kaduna daga garin Warri, jihar Delta, lokacin da 'yan bindigar suka bude wa motar su wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel