Yan Bindiga Sun Kashe Wani Mutum, Sun Sace Yara 13 a Hanyar Kaduna

Yan Bindiga Sun Kashe Wani Mutum, Sun Sace Yara 13 a Hanyar Kaduna

  • 'Yan bindiga sun kashe wani magidanci mai suna Tijani Amedu tare da yin garkuwa da kananan yara 13 a hanyar Kaduna
  • Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 6 ga watan Janairu, kuma sun nemi naira miliyan 50 kudin fansar yaran
  • Kani ga wanda aka kashen, Rasaq ya ce dan uwan nasa da yaran suna hanyar komawa Kaduna daga Warri, jihar Delta lamarin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani magidanci mai suna Tijani Amedu, tare da yin garkuwa da ‘yan uwansa 13, wadanda galibi yara ne, a yankin Katari da ke jihar Kaduna.

Dan uwan mutumin, Rasaq, a wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar The Punch a ranar Laraba, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Tsageru sun farmaki motar kamfen mataimakin gwamnan PDP, sun tafka mummunar ɓarna

Yan bindiga sun kashe wani mutum a hanyar Kaduna
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe wani mutum a hanyar Kadua, sun sace yara 13. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yan bindiga sun tare motar fasinjoji a hanyar Kaduna

Rasaq ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dan uwan nasa tare da iyalansa sun je Warri, jihar Delta ne yin hutun bikin sabuwar shekara, suna hanyar komawa gida Kaduna aka yi garkuwa da su bayan da aka bude masu wuta.
"An sanar da ni cewa motar farko ta samu damar wucewa, amma mota ta biyu ce 'yan bindigar suka tare, kuma ita ce dan uwana da kananan yara kusan 13 suke ciki."

Abin da ya jawo mutuwar Tijani Amedu

Ya ce daga baya ne ‘yan uwan suka san lokacin da yaran suka fara yin magana daga hannun masu garkuwa da mutanen.

A cewar Tori News, yaran ne suka bayyana cewar, an bugi kan babban yayana kuma ya fadi (wanda ya kai ga mutuwarsa), kuma su nemi naira miliyan 50 kudi fansar yaran.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue

"Mun gano gawar dan uwana a ranar Asabar kuma mu binne shi washegari, 7 ga watan Janairu."

A cewar Rasaq.

Rasaq ya ce ya yi magana ta karshe da masu garkuwa da mutanen a ranar Talata.

Hukuncin Kotun Koli: 'Yan sanda sun kama mutum biyar a Kano

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutum biyar da suka tayar da tarzoma a garin Gaya bayan hukuncin Kotun Koli a ranar Juma'a.

Haka zalika rundunar ta ce mutum biyu ne aka ji wa raunuka yayin gangamin murnar hukuncin kotun, kuma tuni aka garzaya da su asibitin Gaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel