An Samu Bayani, Jami'a Ta Faɗi Adadin Daliban da Suka Mutu Ana Bikin Kammala Karatu

An Samu Bayani, Jami'a Ta Faɗi Adadin Daliban da Suka Mutu Ana Bikin Kammala Karatu

  • Jami’ar Nsukka (UNN) ta tabbatar da mutuwar ɗalibanta huɗu bayan wani bikin murna da aka gudanar a wajen harabar jami’ar
  • Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Simon Ortuanya, ya ce ɗalibai 10 ne suka halarci bikin, inda shida ke karɓar magani a asibitoci daban-daban
  • Jami’ar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku tare da dakatar da dukkan ayyukan karatu da sauran harkokin jami’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Enugu – Jami’ar Nsukka (UNN) da ke jihar Enugu ta tabbatar da mutuwar ɗalibanta huɗu bayan sun halarci wani bikin murna da aka gudanar a wajen harabar jami’ar.

Haka kuma, jami’ar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin girmama ɗaliban da suka rasu sakamakon lamarin.

Daliban jami'ar UNN 4 sun mutu
Sufeta-janar na ƴan sanda a Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Rilwan Disu.
Source: Facebook

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Simon Ortuanya, ne ya tabbatar da aukuwar lamarin yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, kwana guda bayan faruwar al’amarin, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027

Yadda ɗalibai huɗu suka mutu bayan bikin

Farfesa Ortuanya ya bayyana cewa ɗalibai 10 na jami’ar ne suka halarci bikin da aka shirya domin murnar kammala jarabawar shekarar ƙarshe ta ɗaya daga cikin abokansu.

Sai dai ya ce huɗu daga cikinsu sun mutu bayan an yi zargin sun sha wasu abubuwa da ake zargin giya da ƙwayoyin maye ne.

Ya ƙara da cewa sauran ɗalibai shida da suka tsira daga lamarin na karɓar magani a asibitoci daban-daban.

Mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana rasuwar ɗaliban a matsayin babban rashi ga jami'ar, yana mai cewa wannan mutuwar ta yi yawa. UNN ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku

Bayan faruwar lamarin, Ortuanya ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin nuna alhini da girmama ɗaliban da suka rasu.

A lokacin zaman makokin, jami’ar za ta dakatar da dukkan ayyukan karatu da sauran harkokin zamantakewa da ake gudanarwa a makarantar.

Dalibai sun mutu a jami'ar UNN
Kofar shiga jami'ar UNN da ke jihar Enugu a Kudancin Najeriya. Hoto: UNN.
Source: UGC

Matakan da jami'ar ta dauka

Kara karanta wannan

An rasa rayukan mutane yayin jana'iza, da yawa sun raunata a Niger

Haka kuma, ya sanar da dakatar da wani taron tattaunawa da aka shirya gudanarwa tsakanin al'ummar jami'ar da gwamnan jihar Enugu, cewar TheCable.

Ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan ɗaliban da suka mutu, abokansu da sauran al'ummar jami'ar, yana mai cewa jami'ar na tare da su a wannan lokaci na jimami. An yi ƙarin bayani kan sashen da ɗaliban suka fito

Mataimakin shugaban jami'ar ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa dukkan ɗaliban da lamarin ya shafa sun fito ne daga sashen ilimin harhada magunguna.

Ya bayyana cewa ɗaliban sun fito ne daga sassa daban-daban na jami'ar, ba daga sashe guda ba.

Ortuanya ya sake jaddada dokar da jami'ar ta kafa ta haramta bukukuwan sign-out, inda ya buƙaci ɗalibai su guji duk wani abu da ka iya jefa rayuwarsu cikin haɗari.

Ya ce ya kamata kammala karatu ya zama lokacin yin tunani kan makomar rayuwa, ba lokacin gudanar da bukukuwan da ba a kula da haɗarinsu ba.

Jami'a na binciken musabbabin mutuwar ɗaliban

A ƙarshe, mataimakin shugaban jami'ar ya ce suna aiki tare da jami'an tsaro domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar ɗaliban.

Kara karanta wannan

Yadda daliban jami'a 7 suka rasu ana tsaka da bikin kammala karatunsu

Ya ce har yanzu ana gudanar da bincike domin tabbatar da musabbabin aukuwar lamarin.

Ɗalibai sun yi wa abokindu dukan tsiya

A baya, an ji cewa wasu dalibai hudu da ba a bayyana sunayensu ga manema labarai ba sun kashe abokin karatunsu ta hanyar lakada masa duka.

Rahotanni sun ce dalibin ya gamu da ajalinsa ne bayan da abokan hudu suka kama shi yana nadar bidiyon su, lamarin da ya ja suka duke shi.

Jami’in hulda da jama’a na 'yan sanda, Toun Ejire-Adeyemi (DSP), ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da fadin matakin da aka dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.