Matatar Dangote Ta Kafa Tarihi bayan Kammala Sayar da Hannayen Jari
- Matatar Dangote ta kammala sayar da hannayen jari ga jama’a, inda ta samu masu zuba jari daga ƙasashen duniya
- Aliko Dangote ya bayyana cewa kuɗin da aka tara sun haura burin dala biliyan 1.6 da aka sanya, har sau uku ko huɗu
- Matatar tana tace ganga 700,000 na ɗanyen mai kullum, kuma tana shirin ƙara ƙarfin aikinta zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
ABUJA - Wata matatar mai da ke Najeriya, mallakar hamshakin attajirin Afirka, Aliko Dangote, ta kammala sayar da hannayen jari ga jama’a.
An bayyana shirin a matsayin mafi girma a tarihin Afirka, tare da samun masu zuba jari daga ƙasashe 120.

Source: Getty Images
Yaushe aka rufe sayar da hannun jari?
An tsara kammala sayar da hannayen jarin matatar man fetur ta Dangote da ke Legas a ranar 13 ga Oktoba, cewar Vanguard.
Sai dai kamfanin ya ƙara wa’adin da makonni biyu domin bai wa ƙarin ’yan Afirka damar shiga.
Kamfanin bai bayyana adadin kuɗin da aka samu daga sayar da hannayen jarin ba, duk da cewa ya ce burinsa shi ne tara dala biliyan 1.6.
Sai dai Aliko Dangote ya bayyana a farkon wannan watan cewa kuɗin da aka tara sun haura burin da aka sanya da fiye da sau uku ko huɗu.
Ya ce:
“Wannan wata gagarumar nasara ce ta tarihi ga Afirka. Ta nuna abin da zai yiwu idan muka yi imani da nahiyarmu, muka yi aiki tare, sannan muka zuba jari domin makomar da muke da ita tare,” in ji shi a cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Talata.
Matatar mai ta Dangote tana da ƙarfin tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana, kuma tana da burin ninka wannan adadi zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana. Idan hakan ya tabbata, za ta iya zama matatar mai mafi girma a duniya, inda za ta zarce matatar Jamnagar da ke Indiya.

Kara karanta wannan
Tallafin mai: ADC ta sake albishir ga Ƴan Najeriya kan shirin Atiku bayan hawa mulki
Kamfanin ya ce masu zuba jari daga dukkan ƙasashen Afirka 54 da wasu nahiyoyi biyar sun shiga sayar da hannayen jarin.
A watan Yuli, matatar ta samu jarin dala biliyan 2.5 daga masu zuba jari masu zaman kansu.
A watan da ya gabata, kamfanin ya fara aikin gina wata matatar mai da aka tsara za ta lakume dala biliyan 16 a tsibirin Lamu na ƙasar Kenya. Ana sa ran matatar za ta iya tace ganga 700,000 a kowace rana.
A halin yanzu, Afirka tana shigo da sama da kashi 70 cikin 100 na man fetur ɗin da take amfani da shi bayan an tace shi, a cewar wani rahoton Hukumar Kuɗi ta Afirka (AFC) da aka fitar a watan Afrilu. Meta Description
Gwamna ya sayi hannun jari jarin Dangote
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Zamfara ta amince da shirin bai wa mazauna jihar 36,176 hannun jari a rukunin kamfanonin Dangote domin bunƙasa tattalin arziƙi.
Kowane wanda zai amfana ana sa ran zai samu kusan hannun jari 20 ta hanyar shirin sayar da hannun jarin matatar Dangote ga jama’a.
Za a zaɓi waɗanda za su amfana daga ƙananan hukumomi 14 na jihar, inda Gusau za ta samu kaso mafi yawa na mutane 4,522.
Asali: Legit.ng
