"Adadin Mutanen da Suka Sayi Hannun Jari a Matatar Dangote ba Su Kai Yadda Aka So ba"
- Aliko Dangote ya bayyana cewa tayin hannun jarin matatar mansa bai cimma burin jawo masu zuba jari miliyan 10 ba
- Sai dai ya ce tayin ya samu gagarumar karɓuwa daga miliyoyin mutane duk da ƙarancin lokacin da aka ba da dama
- Rahoto ya nuna cewa an samu wadanda suka nemi sayen hannun jari ta Naira tiriliyan 6.4, kusan ninki uku na adadin da aka yi niyyar sayarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya yi bayani kan shirin sayar da hannun jarin matatar mansa da aka kammala kwanakin baya.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Matashin da ya auri mata 2 rana 1 ya rasu a wani yanayi mai cike da al'ajabi
Dangote ya ce tayin sayar da hannun jarin farko ga jama’a (IPO) na ɓangaren kasuwancin matatar mansa bai cimma burin samun masu zuba jari miliyan 10 ba.

Source: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa attajirin ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara na 25 na ƙungiyar Women in Management, Business and Public Service (WIMBIZ), wanda aka gudanar a Legas.
Mutane nawa suka saya hannun jarin?
Sai dai duk da rashin kai wa wannan buri, Dangote ya ce tayin ya jawo hankalin “miliyoyin masu zuba jari”.
Ya ce har yanzu ba a tantance a hukumance yawan mutanen da suka zuba jarin ba, amma ya danganta rashin cimma burin da ƙarancin lokacin da aka ba da damar sayen hannun jarin da kuma matsalolin da wasu suka fuskanta wajen shiga shirin.
Dangote ya ce:
“Ba za mu iya faɗin adadin a yanzu ba domin har yanzu ba mu bayar da rahoto kan hakan ba, amma mun samu gagarumar buƙata daga mutane daban-daban.”
"Idan ka duba, babban adadin masu hannun jari da suka shiga irin wannan tayin a nan, ina ganin GTBank ne. Lokacin da suka gudanar da nasu, mutane 200,000 ne suka shiga. Amma mu muna magana ne kan miliyoyin mutanen da suka shiga.”
Dangote ya kama hanyar kafa tarihi
Dangote ya ce yawan mutanen da suka shiga tayin hannun jarin abin lura ne idan aka kwatanta da wasu manyan tayin hannun jari da aka gudanar a Afirka da sauran sassan duniya.
“Ko a Kenya, Safaricom ce ta fi kowace kamfani samun masu sayen hannun jari amma adadin bai kai 900,000 ba. A duk duniya, Saudi Aramco ta samu kusan miliyan biyar. Don haka ina da tabbacin ba mu yi nisa da wannan adadin ba.”
Dangote ya ce dalilan da suka hana kamfanin cimma burin samun masu zuba jari miliyan 10 sun haɗa da ƙarancin lokaci da kuma rashin sanin yadda wasu mutane za su shiga.

Source: Facebook
Ya kara da cewa:
“Ba mu kai miliyan 10 ba saboda ƙarancin lokaci, kuma mutane da dama ba su san yadda za su shiga su nemi sayen hannun jarin ba.
“Amma wannan ya nuna amincewar da jama’a suka fara yi wa harkokin kasuwanci na kamfanonin da suke hannun jama’a a yau a Afirka. Wannan ne ya sa mutane suka fara fitar da kuɗinsu daga ƙarƙashin katifunsu domin su zuba jari.”
Matatar Dangote ta kafa tarihi
Kun ji cewa matatar Dangote ta kammala sayar da hannayen jari ga jama’a, inda ta samu masu zuba jari daga ƙasashen duniya
Aliko Dangote ya bayyana cewa kuɗin da aka tara sun haura burin Dala biliyan 1.6 da aka sanya, har sau uku ko huɗu.
Asali: Legit.ng

