Ilmin Mata: Wata Kungiya mai zaman kan-ta ta ta jinjinawa El-Rufai

Ilmin Mata: Wata Kungiya mai zaman kan-ta ta ta jinjinawa El-Rufai

Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta maida karatun Boko ya zama kyauta a kaf fadin Jihar Kaduna ga Matan da ke mataki na Sakandare. Wannan yunkuri dai zai taimakawa karatun Mata a Jihar matuka.

Ilmin Mata: Wata Kungiya mai zaman kan-ta ta ta jinjinawa El-Rufai
An jinjinawa El-Rufai na sawwake karatun mata a Kaduna
Asali: UGC

Kungiyar CGE wanda cibiya ce da ke kokarin inganta ilmin Boko ga ‘Ya ‘ya mata a Jihar Kaduna da sauran bangarorin Arewacin Najeriya ta jinjinawa wannan mataki da Gwamna Nasir El-Rufai ya dauka na daukewa 'Yan mata kudin Makaranta.

Gwamnatin Kaduna dai za ta warewa ‘Yan mata da ke karatu a Makarantun Sakandare na Gwamnati kudi har Naira Miliyan 143 a matsayin kudin makaranta a kowane zango. Kwamishinan ilmi na Jihar Malam Jafaru Sani ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Tarihin tutar Najeriya da ma'anar kalolon jikinta

Cibiyar ta CBE ta bayyana cewa matsalar biyan kudin Makaranta yana cikin dalilan da su ke hana mata cigaba da karatu a Jihar. Kungiyar ta CGE dai tana da rajin ganin ‘Ya ‘ya mata sun yi nisa ne a karatun Boko domin su cin ma burin su a rayuwa.

A wani jawabi da Kugiyar ta fitar kwanan nan wanda ya shigo hannun NAIJ Hausa, an nemi sauran Jihohi musamman na Arewa su yi koyi da Gwamna El-Rufai wajen inganta karatun Boko. Kungiyar dai ta horas da mata sama da 8, 500 kawo yanzu.

Kwanakin kun ji cewa Gwamnatin Nasir El-Rufai ta samawa Matasa 257000 aiki a Jihar Kaduna. Gwamnatin ta Jihar Kaduna ta tayi wannan ne duk a cikin shekara 3 da tayi a kan mulki inji Gwamnan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel