Ana Zargin za a yi Gagarumar Tarzoma a wajen Kamfen din Tinubu a Kebbi
- Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa wasu mutane na shirin haddasa rikici a Kebbi ta hanyar amfani da rigunan jam’iyyar wajen nuna cewa mambobinta ne suka aikata hakan
- Jam’iyyar ta ce ta gano shirin raba wa wasu bata-gari rigunan da ke dauke da tambarin ADC domin su tada tarzoma yayin ziyarar Shugaba Bola Tinubu a jihar
- ADC ta bukaci jami’an tsaro da al’umma su kula da lamarin, tana mai cewa ba za ta dauki alhakin duk wani rikici da aka haddasa da sunanta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa akwai wani shiri na amfani da wasu bata-gari wajen haddasa rikici a jihar Kebbi yayin ziyarar da Shugaba Bola Tinubu zai kai jihar.
Jam’iyyar ta ce ta gano wani yunkuri na raba rigunan da ke dauke da tambarin ADC ga wasu mutane domin su haddasa tarzoma, tare da dora laifin kan mambobinta.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar, Atiku Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce shirin na da manufar bata sunan ADC a idon jama’a.
ADC ta gargadi jami’an tsaro
Atiku Abubakar ya ce jam’iyyar ta fito fili ta sanar da al’umma da hukumomin tsaro game da zargin shirin, domin daukar matakan da suka dace kafin ziyarar shugaban kasa.
Ya ce duk wanda aka kama yana aikata barna da sunan ADC bai kamata a dauke shi a matsayin mamban jam’iyyar ba, kuma a hukunta shi bisa tanadin doka.
A cewarsa, jam’iyyar na da mambobi masu mutunci da son zaman lafiya, don haka ba ta goyon bayan duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye.
Ya bukaci mambobinta su kasance masu bin doka da oda kafin ziyarar Tinubu, yayin ziyarar da kuma bayan kammalawarta.
Kebbi ta shirya tarbar Tinubu
A wani bangare kuma, gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaba Bola Tinubu, wanda zai kai ziyara ta kwana daya jihar ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Yakubu Ahmed-BK, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Birnin Kebbi.
Ya ce Gwamna Nasir Idris ya kaddamar da kwamitoci daban-daban domin tsara yadda za a gudanar da ziyarar da kuma gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC.

Source: Facebook
Kwamishinan ya ce shirye-shiryen sun hada da shugabannin APC, zababbun wakilai, mata, matasa, manoma, kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 21 na jihar.
Amaechi ya ce za su yi nasara
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin dan takarar shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsu na samun goyon bayan jihohi 13 a Arewa.
Amaechi ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ADC za ta kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, yana mai cewa jam’iyyarsu na kokarin samun karbuwa a Kudu.
A wani gangamin yakin neman zaben ADC da aka gudanar a jihar Bauchi, tsohon gwamnan jihar Rivers ya yi hasashen cewa jam’iyyar za ta samu nasara a jihohin Neja, Kogi da Nasarawa.
Asali: Legit.ng

