Zamfara: ’Yan Bindiga Sun Shiga Wani Ahali, Sun Hallaka Mutane 12
- ’Yan bindiga sun kashe mutane 12 a iyali guda bayan sun cinna wa ɗakin da suka ɓuya wuta a Jihar Zamfara
- Harin ya faru ne a ƙauyen Gidan Taba da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
- Maharan sun kuma sace wasu mazauna yankin, amma ’yan sa-kai sun samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Maradun, Jihar Zamfara - Wasu ’yan bindiga sun hallaka mutane 12 a iyali guda a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Gidan Taba da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
Maharan sun kai harin ne a daren Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, a unguwar Dosara Birnin Kaya, inda suka farmaki iyalan wani mutum mai suna Mallam Muhammadu Sani.
Wani mazaunin yankin da ya zanta da jaridar Daily Trust ya ce iyalan sun shiga wani ɗaki tare da kulle kansu domin guje wa sace su da maharan ke yi.

Source: Original
Sai dai bayan ’yan bindigar sun gano inda iyalan suke, sun umarce su da su buɗe ƙofar ɗakin. Bayan sun ƙi, maharan suka cinna wa ɗakin wuta.
Shugaban karamar hukumar ya tabbatar
Shugaban Ƙaramar Hukumar Maradun, Sanusi Ahmed Dosara, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana harin a matsayin abin takaici da rashin imani.
Ya ce mutanen da suka mutu sun haɗa da mahaifin iyalin, matansa da ƙananan yaransa a lamari mai cike da alhini.
Dosara ya bayyana cewa ba wai wutar ta cinye gawarwakin mutanen kai tsaye ba ne, amma zafin da ya tashi bayan an cinna wa ɗakin wuta ne ya yi sanadin mutuwarsu.
Ya ce:
“Abin da ya faru a ƙauyen Gidan Taba abin takaici ne da ban tausayi. Mahaifi, matansa da ƙananan yaransa, mutum 12 kenan, duk sun mutu sakamakon wutar.”
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma jagoranci sallar jana'izar waɗanda suka rasu a safiyar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yan bindiga sun tare magidanci da ya ɗauko gawar matarsa daga jihar Kano
An sace wasu mazauna
Baya ga kashe mutane 12, maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mazauna ƙauyen, amma har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka tafi da su ba.
Dosara ya ce wasu ’yan sa-kai sun samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sace bayan sun yi arangama da ’yan bindigar.
Ya ce:
“Ɗaya daga cikin ’yan sa-kai ya tabbatar min cewa ’yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mutane, amma sun tare su tare da kuɓutar da wasu bayan musayar wuta.”
Ya ƙara da cewa yanayin tashin hankali a yankin ya sa har yanzu ba a iya tantance ainihin adadin mutanen da aka sace ba.
An nemi kara tsaro a yankin
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce maharan sun riƙa harbe-harbe ta wurare daban-daban domin rikitar da jami’an tsaro da ɓoye inda suke.
Ya bayyana cewa ya ziyarci sansanin ’yan sandan tafi-da-gidanka mafi kusa da yankin domin ƙarfafa haɗin gwiwa kan tsaro da kuma hana sake kai irin wannan hari.

Kara karanta wannan
Malamin musulunci ya yi magana, ya fadi yadda yan bindiga suka sace mata a gonarsa
Lamarin ya ƙara jawo hankalin jama'a kan matsalar rashin tsaro a wasu sassan Jihar Zamfara, musamman yankunan da ke kusa da babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto.
Al'ummomin yankin sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayukan jama'a da kuma dakile hare-haren ’yan bindiga.
Asali: Legit.ng
