Jirgin Ruwa Dauke da Kwamishina, Jami'in NSCDC da Wasu Mutane Ya Yi Hatsari
- Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya tare da hadin gwiwar masu kamun kifi sun ceto fasinjoji bakwai bayan jirgin ruwansu ya gamu da hatsari a Bayelsa
- Cikin wadanda aka ceto har da Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari na jihar Bayelsa, Ebieri Jones
- Wani dan sanda ne kadai ya bace har yanzu ba a gansa, yayin da ake ci gaba da aikin nema a cikin kogin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Baylesa, Nigeria - Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, tare da hadin gwiwar wasu kamun kifi na Abedigbene a Jihar Bayelsa, ta ceto fasinjoji bakwai daga nutsewa bayan wani jirgin ruwa da suke ciki ya gamu da hatsari.
Cikin wadanda aka ceto har da Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari na Jihar Bayelsa, Ebieri Jones, wani jami’in hukumar tsaro da kare fararen hula ta Najeriya (NSCDC), da wasu fasinjoji biyar.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Matashin da ya auri mata 2 rana 1 ya rasu a wani yanayi mai cike da al'ajabi

Source: Facebook
Premium Times ta rahoto cewa hakan na kunshe ne cikin rahoton ayyukan rundunar da Daraktan Yada Labarai na Sojin Ruwa, Abiodun Folorunsho, ya fitar, a Abuja.
Folorunsho ya ce jami’an sansanin Forward Operating Base (FOB) FORMOSO ne suka gudanar da aikin ceto tare da hadin gwiwar masu shiga ruwa na yankin a kogin Abedigbene da ke Karamar Hukumar Brass.
Ya bayyana cewa jirgin ruwan fasinjojin yana kan hanyarsa ne daga Yenagoa zuwa Akassa, kuma rahotanni sun nuna cewa mutane takwas ne ke cikinsa.
Yadda aka gudanar da aikin ceto
“Lamarin ya shafi wani jirgin ruwan fasinjoji da ke tafiya daga Yenagoa zuwa Akassa, wanda rahotanni suka nuna cewa yana dauke da mutane takwas.
“Bayan wani masunci ya bayar da rahoton neman agaji, jami’an da aka jibge a Labrador Lagosgbene sun gaggauta tattara kayan aiki zuwa wurin, inda suka fara aikin bincike da ceto.
“Tare da taimakon al’ummar yankin, an gano wadanda suka tsira sannan aka kai su sansani, inda aka ba su agajin gaggawa. Binciken farko ya nuna cewa babu wanda ke da raunin da ake iya gani,” in ji shi.
Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa wani fasinja da aka bayyana a matsayin dan sanda ne kadai ya bace. Ya tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin bincike da ceto domin gano inda jami’in yake.
Kwamishina ya tsallake rijiya da baya
Ya ce an kai kwamishinan da sauran mutane shida da suka tsira zuwa Yenagoa domin su sake haduwa da iyalansu.

Source: Original
Ya ruwaito Kwamandan FOB FORMOSO, Sunday Haruna, yana yabawa jami’an rundunar bisa gaggawar da suka yi wajen kai dauki da kuma kwarewar da suka nuna yayin gudanar da aikin.
Haruna ya kuma yaba da gudummawar da masunta na yankin da sauran al’ummar da ke zaune a yankin suka bayar wajen nasarar aikin.
Jirgin ruwa ya yi ajalin mutane a Benue
Kun ji cewa hukumar SEMA ta jihar Benuwai ta tabbatar da mutuwar fasinjoji sama da 30 a hatsarin jirgin ruwa a mashigar Buruku.
Jirgin ruwan na gargajiya wadda aka hada da katako ya kife ne yankin mashigar Buruku da ke kogin Katsina-Ala, a Karamar Hukumar Buruku ta jihar Benuwai.
Asali: Legit.ng
