Neman Gado Ya Sa Wata Mata Kitsa Kashe 'Ya'yan Kishiyarta 4 a Kano

Neman Gado Ya Sa Wata Mata Kitsa Kashe 'Ya'yan Kishiyarta 4 a Kano

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wata mata mai shekara 20 da wasu mutum uku bisa zargin sacewa da kashe wani yaro mai shekara 14
  • ’Yan sandan sun ce matar ta kitsa kashe ’ya’yan kishiyarta hudu domin danta tilo shi kadai ya gaji dukiyar mahaifinsu a nan gaba
  • An gano cewa matar ta dauki nauyin kisan ne duk da cewa mijinta, wanda shi ne mahaifin yaran, yana raye bai riga ya mutu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wata mata mai shekara 20 da wasu mutum uku bisa zargin hannu a sacewa da kashe wani yaro mai shekara 14, a wani shiri da ake zargin an kitsa domin kawar da ’ya’yan kishiyarta.

Rahoto ya ce matar da ake zargi da jagorantar kitsa laifin ita ce Hajiya Rukayya Auwal, mai shekara 20, mazauniyar unguwar Mararaba da ke karamar hukumar New Karu a jihar Nasarawa.

Matar da aka kama a Kano
Mutanen da aka kama a Kano kan kashe dan kishiya. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kakakin rundunar a jihar Kano, CSP Abdullahi Kiyawa ne ya wallafa hakan a wata sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Yadda aka kashe yaro 1

A cewar sanarwar, mahaifiyar yaron mai suna Mahmoud Auwal, mai shekara 14, ta kai rahoton bacewarsa ga ’yan sanda a ranar 29 ga Afrilu, 2026.

’Yan sandan sun ce an yaudari yaron ne aka jawo shi zuwa hannun wadanda ake zargi tun kwanaki tara kafin mahaifiyarsa ta kai rahoton bacewarsa.

Bayan samun korafin, tawagar yaki da masu garkuwa da mutane ta rundunar ta fara bincike, inda ta kama Muhammad Musa Isma’il, mai shekara 20, a ranar 3 ga Nuwamba.

Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya yaudari yaron tare da jan hankalinsa a ranar 20 ga Afrilu, 2026, da misalin karfe 12:30 na rana.

Isma’il ya kuma ambaci wasu mutum biyu, Abubakar Muhammad Isah, mai shekara 27, da Auwal Muhammad, mai shekara 26, a matsayin wadanda suka taimaka masa.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

’Yan sandan sun ce wadanda ake zargin sun hada baki ne wajen kashe yaron, sannan suka bar gawarsa a wurin da suka aikata laifin.

Daga bisani, jami’an sashen ’yan sanda na Kwalli sun gano gawar tare da kai ta dakin ajiyar gawa na Asibitin Kwararru na Sir Muhammad Sunusi.

Batun kitsa kashe ’ya’yan kishiya

Rundunar ta ce ci gaba da bincike ya kai ga kama Rukayya, bayan sauran wadanda ake zargin sun nuna cewa ita ce ta umurce su da aikata laifin.

A cewar sanarwar, bincike ya nuna cewa Rukayya kishiyar mahaifiyar yaron ce, kuma ana zargin ta kitsa kawar da dukkan ’ya’yan mijinta hudu domin danta tilo shi kadai ya gaji dukiyar mahaifinsu a nan gaba.

’Yan sandan sun jaddada cewa mijin nata, wanda shi ne mahaifin yaran, yana raye a lokacin da ake zargin an kitsa wannan mummunan shiri.

Haka kuma, rundunar ta yi zargin cewa Rukayya ta dauki hayar wasu ’yan daba domin su kai wa Isma’il hari a Mararaba, karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, da nufin hana shi tona asirin laifin.

An kama 'yan daba a Kano

A wani labarin, mun rahoto cewa rundunar ’yan sandan Kano ta kama mutum takwas bayan rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da NDC a karamar hukumar Bichi ta jihar.

Rundunar ta ce mutum biyar sun jikkata, yayin da aka lalata motoci 13 a rikicin da ya faru da misalin karfe 4:45 na yammacin ranar Lahadi.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce jami’an ’yan sanda sun gaggauta zuwa wurin bayan samun rahoton lamarin, inda suka dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng