An Kama Mata Bisa Zargin Sanya Guba a Abincin ’Ya’yan Kishiyarta, Ɗaya Ta Mutu a Jihar Niger
- ’Yan sanda sun kama wata mata mai suna Mariya Abdullahi bisa zargin ba wa ’ya’yan kishiyarta wani abu da ake zargin guba ne
- Ɗaya daga cikin yaran biyu ta rasu, yayin da ɗayar ke karɓar magani a asibiti kamar yadda rahotanni suka bayyana
- Rundunar ’yan sandan Niger ta ce ana ci gaba da binciken matar bayan ta yi ikirarin cewa wata ƙawarta ce ta rinjaye ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Niger - Rundunar ’yan sandan Jihar Niger ta kama wata mata bisa zargin sanya wani abu da ake zargin guba ne a cikin abin da ’ya’yan kishiyarta biyu suka sha, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikin yaran.
Matar mai suna Mariya Abdullahi ta aikata hakan ne a al’ummar Takuti da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Niger.
Yaran da abin ya shafa na da shekaru huɗu da tara. Rahotanni sun nuna cewa sun sha wani abu da ake zargin guba ne daga cikin ƙoƙon da aka ba su.

Source: Original
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Yadda lamarin ya faru
An ruwaito cewa Mariya ta ba yaran abin da ake zargin guba ne bayan wata ƙawarta ta ƙarfafa mata gwiwar yin hakan.
Bayan sun sha abin, yaran sun suma, inda aka garzaya da su wani asibiti da ke kusa da yankin domin samun kulawar likitoci.
Sai dai ɗaya daga cikin yaran ta rasu kafin samun cikakkiyar kulawar asibitin, yayin da aka tura ɗayar zuwa babban asibiti domin ci gaba da jinyarta.
Rahoton ya bayyana cewa har zuwa lokacin da aka wallafa labarin, ɗayar yarinyar tana samun kulawar likitoci.
Abin da ake zargin ya jawo
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Niger, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar 7 ga watan Nuwamba.
Ya ce an kama matar kuma tana amsa tambayoyi a hannun jami’an ’yan sanda a jihar ta Niger da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
A cewar Abiodun, matar ta shaida wa ’yan sanda cewa ta aikata hakan ne saboda ba ta iya haifa wa mijinta ɗa, kuma wata ƙawarta ce ta ingiza ta.
Sai dai wannan bayani na daga cikin ikirarin da ake bincike a kai, kuma har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru.
’Yan sanda sun fara bincike
A bangare guda, kakakin rundunar ya ce za a tura wadda ake zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar (SCID) da ke Minna domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.
Ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda sun samu rahoton lamarin ne a ofishin ’yan sanda na Lapai, inda suka garzaya wurin suka gano yaran biyu.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da bincike kan lamarin domin tabbatar da adalci. Wannan lamari ne da ake samu a tsakanin kishiyoyi a bangarori daban-daban na Najeriya, wand ake jefa yaran da ba su ji ba su gani ba cikin mawuyacin hali.
Asali: Legit.ng

