An Saki Sunayen Ɗaliban Islamiyya 15 da Aka Yi Garkuwa da Su a Neja
- An bayyana sunayen ɗaliban makarantar Islamiya 15 da ’yan bindiga suka sace yayin da suke taimaka wa malaminsu girbin masara a jihar Neja
- Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi shugabannin ƙauyen tare da neman kuɗin fansa sama da Naira miliyan 100
- Malamin ya roƙi gwamnatin jihar Neja da jami’an tsaro su gaggauta kai ɗauki domin ceto yaran da ake zargin suna tsare a wani gini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - An bayyana sunayen ɗaliban makarantar Islamiya 15 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jiharr Neja, yayin da masu garkuwar suka nemi sama da Naira miliyan 100 domin sakin su.
An sace yaran ne a ƙarshen makon da ya gabata lokacin da suke taimaka wa malaminsu, Malam Aminu Bako, girbin masara a gonarsa da ke ƙauyen Tungan-Bako, ƙaramar hukumar Rafi.

Source: Facebook
Malam Bako ne ya bayyana sunayen yaran tare da tabbatar da cewa masu garkuwar sun tuntubi shugabannin ƙauyen domin neman kuɗin fansa, cewar PM News.
An bayyana sunayen ɗaliban Islamiyyar
Malamin ya bayyana cewa yaran da aka sace sun haɗa da Hassana Isah, Aliya Ahmad, Hajara Musa, Hauwa'u Abubakar, Halima Yahaya, Asma'u Jamilu, Radiya Salisu da Aminatu Salisu.
Sauran sunayen sun haɗa da Aisha Bello, Rahinatu Sani, Aminatu Alhassan, Nafisa Ayuba, Bilkisu Adamu, Salaha Abdullahi da Hajara Salisu.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Bako ya nuna damuwa kan yadda yaran ke ci gaba da zama a hannun masu garkuwa, yana mai cewa iyalansu ba su samu cikakken taimako daga hukumomi ba.
Ya ce mukaddashin shugaban ƙaramar hukumar Rafi da shugaban ’yan sanda na sashen yankin su ne kaɗai jami’an gwamnati da suka kai musu ziyara tun bayan sace yaran.

Source: Original
An nemi gwamnatin Neja ta kai ɗauki
A cewar malamin, ’yan sa-kai ne ke jagorantar ƙoƙarin gano inda aka kai yaran, yayin da bayanan sirri ke nuna cewa har yanzu ana tsare da su a cikin jihar Neja.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yan bindiga sun tare magidanci da ya ɗauko gawar matarsa daga jihar Kano
Ya ce:
“Mun ji cewa har yanzu suna cikin jihar Neja, an kulle su a wani gini, wataƙila ba sa samun abinci. Muna cikin damuwa, muna son hukumomi su taimaka mana wajen ceto su.”
Bako ya roƙi jami’an sojoji da su gaggauta shiga lamarin domin ceto yaran, yana mai cewa iyayensu na cikin matsananciyar damuwa.
An nemi sama da Naira miliyan 100
Ɗaya daga cikin iyayen yaran, Malam Adamu, ya bayyana cewa masu garkuwar sun fara tunanin cewa yaran ɗaliban makarantun gwamnati ne, lamarin da ya sa suka nemi kuɗin fansa sama da Naira miliyan 100.
Adamu ya buƙaci gwamnatin jihar Neja ta shiga tsakani domin tabbatar da an ceto yaran, yana mai jaddada cewa bai kamata a bar aikin ga ’yan sa-kai kaɗai ba.
Ya ce:
“Wannan ba lokacin barinmu mu dogara da ’yan sa-kai kaɗai ba ne.”
Malami ya fadi yadda aka sace daliban
Mun ba ku labarin cewa mai makarantar Islamiyya ya ce ya tsallake rijiya da baya bayan ya hango ’yan bindigar suna awon gaba da ɗalibai mata a gonarsa da ke Tungan-Bako.

Kara karanta wannan
Malamin musulunci ya yi magana, ya fadi yadda yan bindiga suka sace mata a gonarsa
Ya bayyana cewa ɗaliban sun je gonar ne domin taimaka masa girbin masara lokacin da maharan suka kai farmaki.
Mahaifin ɗaya daga cikin yaran ya ce ’yarsa mai shekara 12 na cikin waɗanda aka sace, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin ceto su.
Asali: Legit.ng
