Yan Bindiga Sun Sace Mata da Dama a Gonar Malamin Addinin Musulunci a Najeriya
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mata 14 da ke aikin gona a yankin Mekunjeri da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja
- Rahotanni sun nuna cewa asu garkuwa da mutanen sun nemi a samar musu da kayan abinci kafin su saki matan da suka aace
- An ce sun tuntubi malamin addinin Musuluncin da suka aace matan a gonarsa da iyalan waɗanda aka sace domin isar da buƙatarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mata 14 da ke aiki a gonar wani malamin addinin Musulunci a yankin Mekunjeri, da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma buƙaci a ba su kayan abinci a matsayin sharadin sakin matan da suka sace.

Source: Original
Yan bindiga sun tuntubi malamin
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun kai farmaki gonar ne da yammacin ranar Lahadi, inda suka yi awon gaba da matan waɗanda ke da alaƙa da makarantar Islamiyya da malamin ke gudanarwa.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun tuntubi malamin, wanda aka bayyana da sunan Malam, tare da iyalan matan da aka sace.
A yayin tattaunawar, ’yan bindigar sun buƙaci a samar musu da kayan abinci kafin su saki waɗanda suka yi garkuwa da su.
An nemi kayan abinci kafin sakin matan
Buƙatar kayan abincin da maharan suka gabatar ta ƙara jawo damuwa kan halin da matan ke ciki, musamman ganin cewa har yanzu suna hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.
Ba a bayyana irin kayan abincin da ’yan bindigar suka nema ko adadin abin da suke buƙata ba a cikin rahoton da ya fito zuwa yanzu.
Haka kuma, ba a samu ƙarin bayani kan ko an fara wani shiri na ceto matan ko kuma an yi wani yunƙuri na tattaunawa da maharan ba.
Rundunar ’yan sanda ta yi martani
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai bincika cikakken bayani kan lamarin kafin ya yi ƙarin bayani.
“Ku ba ni lokaci in gano cikakken bayani kan lamarin da ya faru sannan in dawo gare ku,” in ji shi.

Source: Facebook
A lokacin haɗa wannan rahoto, ana jiran ƙarin bayani daga rundunar ’yan sandan jihar Neja kan sace matan da kuma matakan da ake ɗauka domin tabbatar da tsaronsu.
Yan bindiga sun sace mata 29 da yaro
Kun ji cewa wasu miyagun ’yan bindiga sun kai hari ƙauyuka huɗu a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja, inda suka sace mata 29 da karamin yaro.
Bayanai daga mazauna yankin sun ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa, ƙarƙashin jagorancin ’yan sanda na caji ofis din Bangi, sun bi sawun maharan jim kaɗan bayan faruwar lamarin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma ceto wasu daga cikin matan.
Asali: Legit.ng

