An Bayyana Mutanen da Ke Amfana da Sauye Sauyen da Tinubu Ya Kawo Najeriya
- Atedo Peterside ya ce masu kuɗi sun samu ci gaba a jarinsu da kuɗaɗen shigarsu, yayin da talakawa ke fama da wahalar samun abubuwan yau da kullum
- Ya bayyana cewa yankunan Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu sun fi fuskantar matsalar talauci
- Peterside ya ce gwamnati ta gaza samar da isassun tsare-tsaren tallafi ga talakawa yayin aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Atedo Peterside, wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC Bank Plc da gidauniyar Anap Foundation, ya yi magana kan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu.
Atedo Peterside ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu sun fi amfani ga masu hannu da shuni, yayin da suka ƙara tsananta halin rayuwar miliyoyin ’yan Najeriya.

Source: Getty Images
Peterside ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamban 2026 yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV.

Kara karanta wannan
"Zan samar da irin Dangote 20 cikin shekara 4"; Dan takarar shugaban kasa ya fadi shirinsa
Dan kasuwar ya ce masu kuɗi sun samu ci gaba a jarinsu da kuɗaɗen shigarsu cikin shekaru uku da suka gabata.
Sai dai ya ce akasin haka ne ke faruwa ga masu ƙaramin ƙarfi, waɗanda ke fama da wahalar biyan buƙatun yau da kullum, ciki har da sayen abinci da biyan kuɗaɗen hidimomi.
Masu kuɗi sun amfana, talakawa na shan wahala
Peterside ya ce idan mutum yana cikin masu matsakaicin ƙarfi zuwa masu hannu da shuni, za a iya nuna masa yadda jarinsa a kasuwar hannayen jari da sauran harkokin zuba jari ya inganta.
Ya bayyana cewa irin waɗannan mutane na iya kasancewa cikin waɗanda suka fi samun ci gaba a cikin shekaru ukun da suka gabata.
Sai dai ya ce mutanen da ba su da isassun kuɗaɗen ajiya, kuma ke fama da wahalar samun abinci, suna cikin mawuyacin hali fiye da da.
A cewarsa, akwai kusan ’yan Najeriya miliyan 100 da ke ƙoƙarin samun ko da abinci sau biyu a rana, tare da wahalar biyan kuɗaɗen buƙatunsu na yau da kullum.
“Idan kana cikin masu matsakaicin ƙarfi zuwa masu hannu da shuni, zan iya nuna maka a allo yadda jarinka a kasuwar hannayen jari da sauran harkokin zuba jari ya inganta.
"Zan iya nuna maka cewa mai irin wannan matsayi ya fi samun ci gaba a cikin shekaru uku da suka gabata. Amma idan kai ma’aikaci ne mai ƙaramin albashi, ba ka da kuɗin ajiya sosai, kuma kana fama da wahalar cin abinci, zan iya nuna maka cewa halinka ya fi muni sosai.” In ji shi.
Ya yi magana kan yawaitar talauci
Peterside ya ce gwamnati ta gaza samar da isassun tsare-tsaren tallafa wa marasa ƙarfi domin rage musu radadin sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa.
Da yake magana kan bayanan shekarar 2025 da TheCable Index ta fitar, ya ce akwai babban bambanci tsakanin matakan talauci a yankunan Najeriya.
Ya bayyana cewa matsalar talauci ta fi kamari a yankunan Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Kudu.
A cewarsa, jihohi kusan 12 ne kawai tare da Babban Birnin Tarayya (FCT) ke da adadin talauci da bai kai kashi 50 cikin 100 ba.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta fara biyan tallafin N50,000 duk wata ga 'yan Najeriya, an ji masu amfana

Source: Facebook
Gwamnatin Tinubu ta raba kudade
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kammala fitar da Naira biliyan 75 ga masu masana'antu 104, yayin da ta raba Naira biliyan 65.8 ga ƙananan 'yan kasuwa 15,018 a faɗin Najeriya.
Gwamnati ta ɗauki matakin ne domin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida, faɗaɗa harkokin kasuwanci da samar da guraben ayyukan yi ga 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng
