Gwamna Dauda Lawal Ya Gayyaci Sarki Sanusi II Bude Masallaci a Zamfara
- Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya karɓi baƙuncin Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda ya jagoranci buɗe Masallacin Zawiyya da aka sabunta a Gusau
- Babban limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, shi ma ya halarci taron inda ya jagoranci sallar Juma’a a masallacin mai dimbin tarihi
- Wasu daga cikin masu amfani da Facebook sun yaba da aikin, yayin da wasu suka yi amfani da damar wajen sukar gwamnatin Zamfara kan matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara – Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karɓi baƙuncin Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II, wanda ya je Gusau domin jagorantar buɗe Masallacin Zawiyya da gwamnatin jihar ta sabunta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya fitar, inda ya ce sabunta masallacin na daga cikin ayyukan inganta wuraren ibada da gwamnatinsa ke gudanarwa.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, gwamnan ya gode wa sarkin bisa halartar taron, tare da yabawa babban limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, wanda ya jagoranci sallar Juma’a a masallacin.
Dauda Lawal ya gode wa Sanusi II
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana farin cikinsa kan ziyarar Sarkin Kano, yana mai cewa halartar taron da ya yi ya nuna karamci da kulawa.
Ya ce sabunta Masallacin Zawiyya na daga cikin shirye-shiryen gwamnatinsa na gyarawa da inganta masallatai a faɗin jihar.
Gwamnan ya kuma roƙi Allah Ya ba da ladan aikin, tare da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.
Maqari ya jagoranci sallar Juma'a
A cikin saƙon nasa, Dauda Lawal ya miƙa godiya ga Farfesa Ibrahim Maqari, babban limamin Abuja, bisa halartar taron da kuma jagorantar sallar Juma’a a masallacin.
Ya bayyana Masallacin Zawiyya a matsayin wurin ibada mai tarin tarihi, wanda aka sabunta domin inganta shi.

Kara karanta wannan
Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso
Jama'a sun yi martani
Wasu masu amfani da Facebook sun bayyana farin cikinsu kan zuwan Sarkin Kano da buɗe masallacin, inda suka yi addu’ar Allah Ya saka wa gwamnan da alheri.
Sai dai wasu sun yi amfani da damar wajen nuna damuwa kan matsalar tsaro da rashin isassun ayyukan raya ƙasa a wasu yankunan Zamfara.

Source: Facebook
Wani mai amfani da Facebook mai suna Mubarak Adam Bukkuyum ya ce al’ummar yankinsu na cikin matsin lamba, yana mai cewa ba su ga isasshen tasirin ayyukan gwamnati a yankin ba.
Haka kuma, wasu sun yi tsokaci kan matsayin Muhammadu Sanusi II, inda suka bayyana shi a matsayin tsohon Sarkin Kano, yayin da wasu suka ci gaba da kiransa da Mai Martaba.
Sanusi II ya caccaki Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Sarki Sanusi II, ya yi gargaɗi kan yawan bashin Najeriya da almubazzarancin kuɗin gwamnati, yana mai cewa suna barazana ga dorewar tattalin arzikin ƙasar.
Sanusi II ya bayyana cewa biyan bashin Najeriya ya cinye kashi 124 cikin 100 na kuɗin shigar gwamnatin tarayya a farkon shekarar 2026.
Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ya kuma buƙaci gwamnati ta fifita wutar lantarki, noma, hanyoyi da fasaha wajen kashe kuɗin ƙasa.
Asali: Legit.ng

