Duniya Labari: Daya Daga Cikin ’Ya’yan Sarki Sanusi I Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An shiga jimami a Kano bayan rasuwar Gali Sanusi, ɗaya daga cikin ’ya’yan marigayi Sarki Muhammadu Sanusi I, bayan fama da jinya
- Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da sallar jana’izarsa ranar Juma’a, 23 ga Oktoba 2026, da ƙarfe 9:00 na safe a fadar Sarkin Kano
- Mutane da dama sun yi ta alhinin rasuwar marigayin, suna addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, tare da ba iyalansa haƙurin jure rashinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An shiga jimami a jihar Kano bayan babban rashi da aka yi a yau na daya daga cikin iyalan sarautar jihar.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar daya daga cikin 'ya'yan marigayi Sarki Muhammadu Sanusi I da ake kira Gali Sanusi bayan fama da jinya.

Source: Twitter
An yi babban rashi a masarautar Kano
Wakilin Legit Hausa ya samu bayanin ne daga shafin Muhammadu Sanusi II Study Snippets wanda ya wallafa a shafin X a yau Juma'a.
Sanarwar ta ce Gali Sanusi ya yi bankwana da duniya bayan bayar da gudunmawa mai tarin yawa a rayuwarsa.
Legit Hausa ta fahimci cewa an gudanar da jana'izarsa a yau Juma'a 23 ga watan Oktobar shekarar 2026 da misalin karfe 9:00 na safe a fadar Sarkin Kano.
Sanarwar ta ce:
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, Gali Sanusi, ɗaya daga cikin ’ya’yan Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi I, ya rasu.
"Za a gudanar da sallar jana’izarsa da ƙarfe 9:00 na safiyar yau a fadar Sarkin Kano.
Allah Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya kuma ba mu haƙurin jure wannan babban rashi. Amin."
Mutane da dama sun yi jimamin mutuwar marigayin inda suke bayyana irin gudunmawar da ya ba al'umma lokacin da ya ke raye a doron kasa.
Hakimin Takai ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, an ji cewa Masarautar Kano ta sanar da rasuwar Alhaji Ibrahim Sani Gaya, Ubandoman Kano u kuma Hakimin Takai, wanda ya rasu yana da shekaru 80 a duniya.
Sanarwar da mai martaba Muhammadu Sanusi II ya fitar ta ce an gudanar da jana'izar marigayin ranar Litinin da misalin karfe 9:00 na safe a gidansa da ke garin Gaya.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, musamman Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, da sauran al'ummar Gaya bisa wannan babban rashi.
Asali: Legit.ng

