An Gano "Bakin Akwati" na Jirgin Rundunar Sojojin Najeriya da Ya Yi Hatsari
- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta gano bakin akwati, watau na’urar nadar muryar matukan jirgi daga tarkacen jirgin ATR-42 da ya yi hatsari
- Mutane 25, da suka hada da ma’aikatan jirgin biyar da fasinjoji 20, sun mutu a hatsarin wanda ya auku a jihar Ondo
- Ana ci gaba da neman sauran bangaren na’urar nadar bayanan tafiyar jirgin domin gudanar da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo, Nigeria - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta gano na’urar nadar muryar matukan jirgi (CVR) wacce ake kira da bakin akwayi daga cikin tarkacen jirginta da ya yi hatsari a Ondo.
Jirgin kirar ATR-42 ya yi hatsari ne a garin Igbokoda, karamar hukumar Ilaje da ke Jihar Ondo, inda dukkan mutane 25 da ke cikinsa suka mutu.

Source: Facebook
Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sa hannu, kuma aka wallafa a shafin rundunar na Facebook.
Rundunar ta kuma gano wani bangare na na’urar nadar bayanan tafiyar jirgin (FDR), yayin da ake ci gaba da kokarin gano da kuma kwato sauran bangaren na’urar.
An gano na’urar nadar murya
Ejodame ya ce tawagogin kwararru daga rundunar sojin sama da Hukumar Binciken Hadurran Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NSIB) sun tabbatar da cewa na’urar nadar muryar matukan jirgin da aka gano tana nan cikakkiya.
Ya ce sauran abubuwan da aka zakulondaga wurin hatsarin sun hada da tarkacen jirgin, wasu sassan injinsa da kuma gawarwakin mutane.
A cewarsa, ana ci gaba da aikin binciken sauran tarkacen jirgin duk da wahalar da ake fuskanta sakamakon kasancewar wurin da hadarin ya faru a cikin fadama.
Ejodame ya bayyana cewa ana gudanar da binciken hadarin cikin taka-tsantsan da kwarewa, domin tabbatar da cewa sakamakon binciken ya kasance cikakke kuma ya dogara da hujjojin da aka samu.
Ana kokarin tantance gawarwakin

Kara karanta wannan
Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamna a 2027, ta umarci a sake zaben fitar da gwani
Kakakin rundunar ya kara da cewa ana kula da gawarwakin mutanen da suka rasu cikin kulawa ta musamman.
Ya ce Sashen Tantancewa da Rarrabewa na NAF ne ke gudanar da matakan da suka dace domin tabbatar da an gano wadanda suka rasu yadda ya kamata.
Ya kuma bayyana cewa rundunar ta ci gaba da tuntubar iyalan mamatan domin sanar da su halin da ake ciki da kuma ba su goyon bayan da ya dace.

Source: Twitter
Baya ga haka, rundunar na tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa kan batutuwan da suka shafi muhalli, wadanda al’ummar yankin da hadarin ya faru suka gabatar.
Ejodame ya bukaci jama’a su yi hakuri, yana mai cewa aikin neman tarkacen jirgin da gudanar da bincike na bukatar lokaci, kulawar kwararru da hadin kai tsakanin hukumomin da abin ya shafa.
NAF ta saki sunayen fasinjojin jirgin
Kun ji cewa Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, NAF, ta tabbatar da mutuwar mutane 25 da ke cikin jirgin ATR-42 mai lamba NAF 931 da ya yi hatsari a Igbokoda, jihar Ondo.
Mutanen sun kunshi ma’aikatan jirgin biyar da fasinjoji 20, inda NAF ta ce har yanzu ba a samu wani mutum da ya tsira daga hadarin ba.
Asali: Legit.ng
