Tinubu Ya Yi Ikirarin Cewa Allah Ya Nuna Masa yadda Zai Daƙile Rashin Tsaro?
- Wani hoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa Tinubu ya ce Allah ya nuna masa yadda zai kawo ƙarshen rashin tsaro
- Bincike ya gano cewa babu wata hujja da ke tabbatar da shugaban ƙasar ya furta kalaman da ake danganta masa
- Bidiyoyin fadar shugaban ƙasa da jawabansa yayin ziyarar Umrah a Saudiyya ba su ƙunshi irin wannan furuci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa babu hujjar da ke tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce Allah ya bayyana masa yadda zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.
Wani hoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa shugaban ƙasar ya bayyana cewa Allah ya nuna masa matakan da zai ɗauka domin kawo ci gaba da kawo ƙarshen rashin tsaro.

Source: Twitter
Hoton ya nuna Tinubu sanye da fararen tufafin Ihrami da Musulmi ke amfani da su yayin gudanar da aikin Hajji ko Umrah, cewar Punch.
Rubutun da ke jikin hoton ya danganta masa da cewa:
"Na yi wa Najeriya addu'a, kuma Allah ya bayyana mini abin da zan yi domin ƙasar ta samu ci gaba tare da kawo ƙarshen rashin tsaro. Yanzu na san abin da zan yi."
Yadda hoton ya bazu a kafafen sada zumunta
A ranar 30 ga Oktoba, wani mai amfani da kafar X mai suna @ayomomojubar ya wallafa hoton, wanda daga baya ya samu karɓuwa a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta.
A ranar 1 ga Nuwamba, mawaƙi kuma mai fafutukar kare haƙƙin jama'a, Charly Boy, shi ma ya wallafa hoton a shafinsa na X.
Binciken CableCheck ya kuma gano cewa wasu masu amfani da X sun wallafa irin wannan ikirari, inda suka danganta kalaman da Tinubu.

Kara karanta wannan
"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027
Rubutun hoton ya ƙara da cewa Tinubu ya san abin da zai yi domin kawo ƙarshen rashin tsaro bayan sake zaɓensa.
Zuwa ranar 5 ga Nuwamba, wannan wallafa ta samu kallon sama da 200,000, sharhi 1,400, sake wallafawa 823 da kuma mutane 902 da suka yi mata alamar so.

Source: Facebook
Abin da binciken ya gano
A yayin tabbatar da sahihancin ikirarin, CableCheck ta duba bidiyoyi da sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar dangane da hirarrakin Tinubu a Saudiyya.
A ranar 30 ga Oktoba, Dada Olusegun, mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, ya wallafa bidiyon da ke nuna Tinubu yana amsa tambayoyin wani ɗan jarida a Saudiyya.
Sai dai binciken bidiyon ya nuna cewa shugaban ƙasar bai furta kalaman da aka danganta masa a hoton da ke yawo ba.
Haka kuma, binciken sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar 30 ga Oktoba bai gano irin waɗannan kalamai ba.
A ranar 2 ga Nuwamba, fadar shugaban ƙasa ta sake wallafa wani bidiyo da ke nuna Tinubu yana amsa tambayoyin ɗan jarida bayan dawowa daga ziyartar Ka'aba.

Kara karanta wannan
Malamin musulunci ya yi magana, ya fadi yadda yan bindiga suka sace mata a gonarsa
Sai dai kalaman da ake danganta wa shugaban ƙasar ba su cikin wannan bidiyo.
Hukuncin binciken da aka gudanar
Binciken ya kammala cewa babu wata hujja da ke tabbatar da ikirarin cewa Tinubu ya ce Allah ya bayyana masa yadda zai kawo ci gaban Najeriya da kuma kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Saboda haka, hoton da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta tare da kalaman da aka danganta wa shugaban ƙasar ba su da sahihiyar hujja.
Tinubu ya dawo Najeriya daga Umrah
An ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Jeddah domin dawowa gids Najeriryan bayan kammala aikin Umrah a birnin Makkah.
Bola Tinubu ya yi addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da wadata a Najeriya Tinubu ya gode wa.
Sarkin Saudiyya da Yarima mai jiran gado bisa karimci da damar shiga cikin Ka’aba domin yin sallah.
Asali: Legit.ng
