Yadda Masu Bankin Wema Za Su Duba Cancantar Samun Tallafin N50,000
- Gwamnatin Tarayya ta buɗe hanyar amfani da lambar USSD ta bankin Wema domin wasu ’yan Najeriya su tantance cancantarsu ga tallafin N50,000
- Masu amfani da ALAT za su iya bincika ko sun cancanci tallafin tare da amincewa da karɓar kuɗin ba tare da amfani da intanet ba
- Gwamnati ta yi gargaɗi ga ’yan Najeriya kan masu damfara, inda ta ce karɓar tallafin kyauta ne ba tare da biyan kuɗin rajista ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da hanyar amfani da lambar USSD ta bankin Wema domin wasu ’yan Najeriya su tantance cancantarsu da karɓar tallafin N50,000.
Tallafin naira 50,000 ɗin yana ƙarƙashin shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI), wanda Ma'aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya ke gudanarwa.

Source: Twitter
Ana ci gaba ba da tallafin N50,000
An tsara shirin ne domin tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu rauni waɗanda tsadar rayuwa ta shafa, cewar Leadership.
Bankin Wema, ta hanyar manhajarsa ta ALAT, na cikin cibiyoyin biyan kuɗi guda biyar da gwamnatin ta amince da su domin rabon tallafin.
Bayanan da aka wallafa a shafin shirin NERSI sun nuna cewa masu amfani da ALAT za su iya tantance cancantarsu ta hanyar USSD ba tare da buƙatar intanet ba.
Yadda masu amfani da ALAT za su tantance cancantarsu
Masu amfani da bankin Wema za su iya bin waɗannan matakai domin gano ko gwamnatin ta zaɓe su cikin waɗanda za su amfana da tallafin.
1. Latsa lambar USSD: Buɗe wajen kira a wayarka, sannan ka latsa 94523# ta amfani da lambar wayar da ka yi wa rajista da bankin.
2. Tantance cancanta: Zaɓi sashen tantance cancanta daga cikin zaɓuɓɓukan da za su bayyana, sannan ka bi umarnin da aka bayar.
3. Amincewa da tallafin: Idan gwamnati ta zaɓe ka, bi umarnin da za su bayyana domin amincewa da karɓar tallafin N50,000.
4. Karɓar kuɗin: Bayan amincewa da tallafin, za a kunna walat ɗin wayarka, sannan a tura maka kuɗin.
5. Tabbatar da kuɗin: Za ka samu saƙon SMS da zai tabbatar maka da shigar kuɗin cikin walat ɗinka.
Waɗanne mutane ne suka cancanci tallafin N50,000?
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tallafin na musamman ne ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi da waɗanda ke cikin mawuyacin hali.
An zaɓi waɗanda za su amfana ne daga bayanan katin shaida na ƙasa da kuma rajistar iyalai masu ƙaramin ƙarfi ta ƙasa.
Shirin ya shafi waɗanda suka cancanta a faɗin jihohin Najeriya da ke yankunan siyasa guda shida, cewar Punch.
Sai dai samun asusun ALAT ba ya nufin kai tsaye mutum ya cancanci karɓar tallafin.
Gwamnati ce ke da alhakin zaɓar waɗanda za su amfana, kuma ba ta buɗe wata hanya ta musamman da mutane za su yi rajista domin samun kuɗin ba.
Haka kuma, an bayyana cewa za a raba kuɗin ne a matakai daban-daban, don haka ba kowa ne zai samu sanarwar karɓar tallafin a lokaci guda ba.

Kara karanta wannan
Tallafin N50,000: Gwamnatin Tarayya ta fitar da ka'idoji 4, ta ja kunnen 'yan Najeriya
Gwamnatin Tinubu ta fara biyan tallafin N50,000
An ji cewa Gwamnatin Tarayya ta fara biyan tallafin N50,000 ga wasu ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.
Shirin na bayar da tallafin ne ga iyalai matalauta da masu rauni a faɗin ƙasar, ta hannun kamfanonin hada-hadar kuɗi na zamani da gwamnati ta amince da su.
Asali: Legit.ng

