Yadda za Ku Karbi Tallafin N50,000 Ta Asusun Moniepoint cikin Sauki

Yadda za Ku Karbi Tallafin N50,000 Ta Asusun Moniepoint cikin Sauki

  • Kamfanin hada-hadar kuɗi na Moniepoint ya fitar da ƙarin bayani kan yadda waɗanda suka cancanci tallafin N50,000 na gwamnatin tarayya za su karɓi kuɗinsu
  • Kamfanin ya bayyana cewa waɗanda suka samu saƙon SMS na sanar da biyan tallafin za su yi amfani da lambar USSD da aka aika musu domin amincewa da karɓar kuɗin
  • Moniepoint ta kuma yi bayani kan abin da mutum zai yi idan ya samu saƙon kuskure yayin amfani da lambar *5573*27#, tare da bayyana lokacin da ake sa ran kuɗin zai shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lagos – Kamfanin hada-hadar kuɗi na Moniepoint ya bayyana ƙarin matakai da waɗanda suka cancanci tallafin N50,000 na gwamnatin tarayya za su bi domin karɓar kuɗinsu.

Kamfanin ya ce waɗanda suka samu saƙon SMS na sanar da biyan tallafin za su yi amfani da lambar da aka turo musu domin amincewa da karɓar kuɗin.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya yi murabus saboda gaza shawo kan matsalolin jama'ar shi

Yadda ake cire tallafin kudi
Moniepoint da tambarin Opay. Hoto: Getty Images
Source: UGC

A cikin bayanin da kamfanin ya fitar, ya kuma yi bayani kan yadda za a magance matsalar da ka iya tasowa yayin amfani da lambar USSD ta *5573*27#.

Ya za a yi idan USSD ta ƙi aiki?

Moniepoint ta ce idan mutum ya danna lambar *5573*27# kuma ya ga saƙon kuskure mai cewa ba a ba shi izinin gudanar da wannan aiki ba, ya kamata ya fara jira na ɗan lokaci kafin ya sake gwadawa.

Kamfanin ya bayyana cewa ana gudanar da bincike kan matsalar, don haka ya kamata mutum ya ba da ɗan lokaci kafin ya sake amfani da lambar.

Sai dai idan mutum ya sake gwadawa karo na biyu kuma ya ci gaba da samun saƙon cewa ba shi da izinin gudanar da aikin, hakan na nufin bai cancanci tallafin ba.

Yadda za a karbi tallafin N50,000

Kamfanin ya bayyana cewa waɗanda suka samu saƙon sanar da biyan kuɗin tallafin za su bi matakai uku domin karɓar kuɗinsu.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamnatin tarayya take so mutum ya yi idan aka tura masa saƙon tallafin N50,000

Mataki na farko shi ne buɗe wayar da ke ɗauke da layin da aka aika wa saƙon SMS, sannan a kira a danna USSD da aka turo a saƙon, misali *5573*27#.

Mataki na biyu shi ne bin umarnin da zai bayyana a fuskar waya domin tabbatar da amincewa da karɓar kuɗin da aka turo.

Bayan mutum ya amince da karɓar kuɗin, zai samu wani saƙon SMS na tabbatar da cewa an kammala tura masa kudin.

Tambarin Moniepoint
Alamar kamfanin Moniepoint. Hoto: Moniepoint
Source: UGC

Yaushe kudin zai shiga asusun mutum?

Moniepoint ta bayyana cewa bayan mutum ya samu saƙon SMS na tabbatar da amincewa da karɓar kuɗin, ya kamata ya jira na wasu sa’o’i kafin kuɗin ya shiga wayarsa.

Kamfanin ya ce ba lallai ne kuɗin ya shiga nan take bayan amincewa ba, don haka masu cin gajiyar tallafin su ba da lokacin da ake buƙata domin kammala aikin.

Kamfanonin da ke raba kudin

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen kamfanonin hada-hadar kuɗi guda biyar da ta amince da su domin gudanar da biyan tallafin Naira 50,000 ga masu ƙaramin ƙarfi.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: Yadda ake duba cancanta da karbar kudin cikin sauki

Kamfanonin za su aika saƙonnin SMS ga waɗanda suka cancanta domin neman izininsu kafin tura kuɗin zuwa asusun bankunansu ko wayoyinsu.

Gwamnati ta kuma yi gargaɗin cewa waɗanda za su amfana ba sa buƙatar neman tallafin, biyan kuɗin rajista ko amfani da wakilai domin karɓar kuɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng