Tallafin N50,000: Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Ka'idoji 4, Ta Ja Kunnen 'Yan Najeriya

Tallafin N50,000: Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Ka'idoji 4, Ta Ja Kunnen 'Yan Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta fitar da ƙa’idoji huɗu da ’yan Najeriya za su bi domin kare kansu daga masu damfara da ke neman cin gajiyar shirin NERSI
  • Ba a buƙatar biyan kuɗi, bayar da PIN, OTP ko lambar sirri, ko zuwa wani ofishi domin samun tallafin N50,000
  • Saƙonnin da suka shafi shirin za su fito ne daga ALAT, MoMo, NairaGram, OPay ko Moniepoint kawai, in ji gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi ’yan Najeriya da su kula da wasu muhimman ƙa’idoji guda huɗu yayin da tallafin N50,000 na shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI) ya fara isa ga waɗanda aka zaɓa.

Gwamnatin ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar masu damfara su yi amfani da shirin wajen yaudarar jama’a, musamman ta hanyar yin kamar su jami’an gwamnati ne ko wakilan shirin.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: Yadda ake duba cancanta da karbar kudin cikin sauki

An ja kunnen 'yan Najeriya kan tallafin N50,000
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kudi 'yan N1,000 Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

A wani bayani da aka wallafa a shafin intanet na NERSI wanda Legit Hausa ta gani gwamnati ta bayyana matakan da ya kamata masu fatan cin gajiyar tallafin su ɗauka domin kare kansu daga masu aikata laifukan damfara.

Ƙa’idoji 4 da gwamnati ta fitar

Ɗaya daga cikin ƙa’idojin ita ce, babu wani mutum da zai nemi a biya shi kuɗi domin a saki tallafin da aka ware wa wani.

Haka kuma, gwamnati ta buƙaci ’yan Najeriya da kada su bai wa kowa lambobin sirrinsu na ATM, OTP ko lambar sirri, ko da kuwa mutumin ya gabatar da kansa a matsayin jami’in shirin ko wakilinsa.

Ƙa’ida ta uku ita ce, saƙonnin da suka shafi shirin NERSI za su fito ne daga kamfanonin ALAT, MoMo, NairaGram, OPay ko Moniepoint kawai.

Gwamnatin ta ce duk wani saƙo da ya fito daga wani mai aikawa daban, amma yana ikirarin cewa yana da alaƙa da shirin, ya kamata a yi watsi da shi.

Kara karanta wannan

Opay, Moniepoint da bankuna 5 da ke tura tallafin N50,000 a Najeriya

Ƙa’ida ta huɗu ita ce, babu buƙatar mutum ya yi rajista, ya biya kuɗi ko ya je wani ofishin gwamnati domin a zaɓe shi cikin waɗanda za su amfana da tallafin.

Yadda za a kare kai daga masu damfara

Gwamnatin ta jaddada cewa shirin NERSI kyauta ne gaba ɗaya, don haka duk wani mutum da ya nemi kuɗi ko bayanan sirri daga mai cin gajiyar tallafin ya kamata a ɗauke shi a matsayin abin zargi.

A cikin gargaɗin, gwamnatin ta ce:

"Idan wani abu ya ba ku shakku, ku dakata sannan ku kira layin taimako kafin ku ɗauki wani mataki.”

Dalilin gargaɗin da gwamnatin ta yi

Wannan gargaɗi ya zo ne sakamakon yadda aka sha samun masu damfara da ke amfani da shirye-shiryen tallafin kuɗi na gwamnatin tarayya wajen yaudarar ’yan Najeriya.

A wasu lokutan baya, masu aikata irin waɗannan laifuffuka sun ƙirƙiri shafukan intanet na bogi, sun aika saƙonnin yaudara, sannan sun yi amfani da sunayen jami’an gwamnati wajen karɓar kuɗi ko bayanan sirrin mutane.

Saboda haka, gwamnatin ta shawarci duk wanda ya samu saƙon da yake zargin cewa na shirin NERSI ne da ya fara tantance sahihancin wanda ya aiko shi.

Kara karanta wannan

Yadda masu Opay za su iya karbar tallafin N50,000 duk wata na gwamnatin tarayya

Ta kuma buƙaci ’yan Najeriya da su kira layin taimako na shirin kai tsaye idan sun samu saƙon da ya tayar musu da hankali, maimakon bin umarnin da ke cikinsa ba tare da tabbatar da sahihancinsa ba.

Gwamnatin Tinubu na bayar da tallafi
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron APC a Kaduna Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Tallafin N50,000: Yadda ake duba cancanta

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fitar da cikakken bayani kan yadda ’yan Najeriya da aka zaɓa domin cin gajiyar tallafin N50,000 za su tabbatar da cancantarsu, amincewa da tayin, karɓar kuɗin da kuma cire shi.

Gwamnatin ta kuma gargaɗi waɗanda za su amfana da shirin da su yi hattara da ’yan damfara da ke ƙoƙarin amfani da damar domin yaudarar mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng