Dama Ta Samu: Opay Ya Bayyana Yadda Masu Kananan Wayoyi Za Su Nemi Tallafin N50,000
- Masu amfani da OPay da ba su da wayoyin zamani za su iya duba cancantarsu ga tallafin N50,000
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin NERSI domin tallafa wa gidajen da ke fama da matsin rayuwa, inda waɗanda suka cancanta za su samu N50,000 duk wata
- Ana zaɓen waɗanda za su amfana daga rajistar masu ƙaramin ƙarfi ta ƙasa da bayanan shaidar zama ɗan ƙasa da aka tantance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - ’Yan Najeriya masu amfani da wayoyin hannu na yau da kullum, waɗanda ba su da damar amfani da intanet, za su iya duba ko sun cancanci tallafin N50,000 na Gwamnatin Tarayya ta hanyar danna USSD na OPay.
Wannan dama za ta bai wa kwastomomin OPay damar amfani da sabis ɗin ba tare da sauke manhajar kamfanin ko samun haɗin intanet ba.

Source: UGC
Legit Hausa ta fahimci cewa gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI) domin tallafa wa gidajen da ke fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.
Yadda shirin tallafin N50,000 yake
A ƙarƙashin shirin, ana sa ran waɗanda suka cancanta za su riƙa karɓar N50,000 duk wata.
Ministan Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a ranar 30 ga Oktoba, inda ya ce gwamnati na aiki da kamfanonin samar da ayyukan kuɗi na zamani da ke da lasisi domin tabbatar da cewa kuɗin sun isa ga waɗanda aka ware musu cikin gaskiya da tsaro.
OPay na cikin kamfanonin da aka amince su rarraba kuɗin tallafin, tare da Moniepoint, ALAT na Wema Bank, MoMo Payment Service Bank da NairaGram.
Yadda masu amfani da OPay za su dub
Masu amfani da OPay waɗanda ba su da wayoyin zamani za su iya amfani da lambar USSD ta *955*20# domin shiga tsarin duba cancantar samun tallafin.
Ga matakan da za su bi:
- Ɗauki wayar da aka haɗa da asusun OPay ɗinka.
- Danna lambar *955*20# ta amfani da lambar wayar da aka yi wa rajistar asusun.
- Bi umarnin da zai bayyana a allon wayarka.
- Zaɓi sashen duba cancantar samun tallafin N50,000 na Gwamnatin Tarayya.
- Idan an zaɓe ka, bi umarnin da aka bayar domin amincewa da tayin tallafin.
- Bayar da izinin da ake buƙata domin a tura maka kuɗin.
Bayan kammala waɗannan matakai cikin nasara, waɗanda aka zaɓa za su samu saƙon tabbatarwa ta SMS bayan an tura kuɗin zuwa asusun ajiyarsu na OPay.
Ba a buƙatar kuɗin data ko haɗin intanet domin amfani da wannan sabis, lamarin da zai sauƙaƙa wa masu wayoyin hannu na yau da kullum.

Source: Facebook
Gargadin gwamnati kan tallafin N50,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta gargaɗi ’yan Najeriya da su kula da wasu muhimman ƙa’idoji guda huɗu kan shirin tallafin N50,000.
Gwamnatin ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar masu damfara su yi amfani da shirin wajen yaudarar jama’a, musamman ta hanyar yin kamar su jami’an gwamnati ne ko wakilan shirin.
Asali: Legit.ng

