Da Gaske INEC Ta Yi Watsi da Nafiu Bala Ta Amince da Bangaren Atiku a ADC?
- Hukumar INEC ta musanta wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta sake amincewa da shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark
- INEC ta bayyana cewa saƙon bogi ne, tare da yin Allah wadai da amfani da tambarin hukumar da hoton Kwamishinanta na ƙasa, Mohammed Haruna
- Hukumar ta buƙaci ’yan Najeriya da su yi watsi da saƙon tare da bin sahihan hanyoyin sadarwarta domin samun bayanai kan ayyukanta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta musanta wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta sake amincewa da shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark.
Hukumar ta bayyana cewa ba ta fitar da sanarwar sake tabbatar da shugabancin ba, tana mai gargaɗin jama’a da su guji amincewa da bayanan da ba su fito daga sahihan hanyoyinta na sadarwa ba.

Source: Facebook
Martanin da INEC ta yi a X ya zo ne bayan wani hoton sanarwa ya bazu a kafafen sada zumunta, kwana guda bayan hukuncin kotu da ya soke shugabancin jam’iyyar na ƙarƙashin David Mark.
Matsayar INEC kan shugabancin ADC
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, INEC ta ce hoton sanarwar da ke ikirarin cewa ta sake amincewa da shugabancin ADC na David Mark ƙarya ne kuma ba daga hukumar ya fito ba.
Hukumar ta bayyana cewa ba ta taɓa fitar da sanarwar da ke tabbatar da shugabancin ba, inda ta ce:
“Domin kawar da duk wani shakku, INEC ba ta fitar da irin wannan sanarwar sake amincewa ba.”
Ta kuma buƙaci jama’a da su yi watsi da saƙon baki ɗaya, tare da dogaro da bayanan da ke fitowa daga shafukanta na hukuma da sauran sahihan hanyoyin sadarwarta.
INEC ta yi karin bayani
INEC ta kuma yi Allah wadai da amfani da tambarinta da hoton Kwamishinan hukumar na ƙasa, Mohammed Haruna, a cikin hoton sanarwar ba tare da izini ba.
Hukumar ta jaddada cewa ba ta amince da amfani da tambarin ta ko hoton jami’inta wajen yaɗa bayanan da ba ta fitar ba.
Ta ce irin wannan amfani da sunanta na iya yaudarar jama’a, don haka ya kamata ’yan Najeriya su tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin su amince da shi ko su yaɗa shi.

Source: Twitter
Martanin INEC ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wadda ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark.
TVC ta ruwaito cewa Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ya bayyana kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark a matsayin wanda bai bi ƙa’ida ba.
Keyamo ya caccaki Atiku
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya yi maraba da hukuncin kotu da ya rusa shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark.
Keyamo ya ce ƙungiyar haɗakar da ta karɓi ragamar jam’iyyar ba ta samu izinin hukumomin ADC ba kafin ta gudanar da sauye-sauyen shugabanci.
A nasa martanin, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da kotu da wasu dabaru domin kawo cikas ga jam’iyyun adawa.
Asali: Legit.ng

