Dama Ta Samu: Kamfani Ya Ware Naira biliyan 20 domin Tallafa wa Matasa Yan Kasuwa a Najeriya
- Hukumar SMEDAN da kamfanin fasaha na Zoho sun ƙaddamar da wani shirin tallafa wa kananan yan kasuwa 25,000 a Najeriya
- Wannan hadin gwiwa ta shirya samar da Naira biliyan 20 domin tallafawa wadannan yan kasuwa da za a zaba
- Shirin zai taimaka wa kananan ‘yan kasuwa wajen gudanar da harkokinsu ta yanar gizo domin bunkasa harkokin kasuwancin su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Samun fasahar zamani mai sauƙi na ci gaba da zama babban ƙalubale ga ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa (MSMEs) a Najeriya.
Hakan ya sa Hukumar Bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i ta Najeriya (SMEDAN) tare da katafaren kamfanin fasaha na duniya, Zoho, suka ƙaddamar da wani sabon shiri da zai amfani ‘yan kasuwa 25,000.

Source: Twitter
Kamfanin Zoho zai samar da N20bn
Leadership ta rahoto cewa a ƙarƙashin yarjejeniyar, Zoho za ta samar da kuɗin amfani da manhajojinta da darajarsu ta kai har Naira biliyan 20 ga ‘yan kasuwa da suka cancanta.
Za a zakulo yan kasuwar ne daga cikinnwaɗanda suke cikin tsarin SMEDAN, domin su samu damar amfani da manhajojin kasuwanci na kamfanin da ake amfani da su ta hanyar yanar gizo.
An tsara shirin ne domin rage matsalar kuɗin da ke hana ƙananan ‘yan kasuwa rungumar fasahar zamani, da inganta yadda suke gudanar da harkokinsu, hulɗa da kwastomomi, lissafin kuɗi, haɗin gwiwar ma’aikata da sauran ayyukan kasuwanci.
Shirin GROW Nigerian na SMEDAN
Haɗin gwiwar ya kuma yi daidai da dabarun SMEDAN na shirin GROW Nigerian, wanda ya mayar da hankali kan shigar da ‘yan kasuwa cikin tsarin kasuwanci na hukuma, samun kuɗaɗen jari, da ƙara ƙwarewa da amfani da fasahar zamani.
Da yake magana kan shirin, shugaban SMEDAN, Charles Odii, ya ce abin da hukumar ta fi mayar da hankali a kai shi ne taimaka wa ‘yan kasuwa su wuce matakin fafutukar tsira zuwa samun ci gaba mai ɗorewa.
“Abin da muka fi mayar da hankali a SMEDAN shi ne tabbatar da cewa ƙananan ‘yan kasuwa sun samu damar wucewa daga neman tsira zuwa samun ci gaba da wadata.
"Hakan na nufin taimaka wa ‘yan kasuwa su shiga tsarin kasuwanci na hukuma, ƙara ƙwarewa, samun sababbin kasuwanni da gina sana’o’in da za su iya yin gogayya,” in ji Odii.
Za a yi wa ‘yan kasuwa rajista
Wannan shiri na zuwa ne a daidai lokacin da SMEDAN ke ci gaba da ƙoƙarin shigar da ƙarin ƙananan ‘yan kasuwa cikin tsarin tattalin arzikin hukuma.
Hukumar tana haɗin gwiwa da Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Najeriya (CAC) domin sauƙaƙa rajistar ‘yan kasuwa 250,000 kyauta.

Source: UGC
Ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa da suka cancanta za su iya amfani da Zoho Wallet Credits wajen samun damar amfani da manhajoji sama da 60.
Haka kuma, Zoho da SMEDAN za su samar wa ‘yan kasuwar da suka shiga shirin horo, taruka na koyarwa, shawarwari kai tsaye kan harkokin kasuwanci da kuma ci gaba da ba su tallafin fasaha yayin da suke amfani da shirin.
An fara rijistar tallafin N50,000
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta hannun hukumar SMEDAN ta sake bude shirin ba da tallafin N50,000 ga kananan 'yan kasuwa a Najeriya.
Shirin na bai wa masu gudanar da kananan sana'o'i da kasuwanci tallafin sau daya na N50,000, wanda ba rance ba ne kuma ba a bukatar a mayar da kudin.
Asali: Legit.ng


