El Rufai Ya Aiko Sako ga Masoya da Magoya kan 'Yan Takarar da Za Su Zaba a 2027

El Rufai Ya Aiko Sako ga Masoya da Magoya kan 'Yan Takarar da Za Su Zaba a 2027

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya umarci magoya bayansa da su zaɓi ’yan takarar ADC a zaɓen shugaban ƙasa, gwamna da sauran muƙamai
  • Hafsat Baba ta ce ƙungiyar za ta samar da kundin bayanan magoya bayan El-Rufai a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna
  • ADC ta nuna damuwa kan matsalar tsaro a Birnin Gwari, Giwa da Millennium City, tare da zargin kama magoya bayan El-Rufai sama da 30

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya umarci magoya bayansa da su zaɓi ’yan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a dukkan matakan zaɓen 2027.

Tsohon gwamnan ya bayar da wannan umarni ne ta hannun mataimakiyar shugaban jam’iyyar ta shiyyar Arewa maso Yamma, Hafsat Baba, yayin wani taron haɗin gwiwar ƙungiyoyin magoya bayansa a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya ji dadin giyar mulki, ya cika baki kan girman jam'iyyar a Najeriya

El-Rufai ya bukaci a zabi ADC
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

El-Rufai ya kuma buƙaci magoya bayansa da su kasance masu haɗin kai, zaman lafiya da bin doka yayin da suke ƙoƙarin jawo goyon bayan jama’a ga ADC gabanin babban zaɓen, cewar rahoton Channels tv.

El-Rufai ya buƙaci a zaɓi ADC

Da take magana a wajen taron, Hafsat Baba ta bayyana cewa umarnin tsohon gwamnan ya shafi zaɓen shugaban ƙasa, gwamna, Majalisar Tarayya da kuma Majalisar Dokokin jihar.

Ta ce umarnin ya shafi dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, inda ta ƙara da cewa an shirya taron ne domin haɗa ƙungiyoyin magoya bayan El-Rufai wuri guda.

A cewarta, haɗuwar ƙungiyoyin za ta taimaka wajen tsara ayyukansu da kuma samar da ingantacciyar hanyar gudanar da kamfen da wayar da kan jama’a gabanin zaɓen.

Mataimakiyar shugabar ADC ta shiyyar Arewa maso Yamma ta kuma bayyana cewa ƙungiyar na shirin samar da kundin bayanan magoya bayan El-Rufai a faɗin jihar.

Ta ce za su riƙa gudanar da tarurruka akai-akai domin ƙarfafa haɗin kai da inganta ayyukan tattara goyon bayan jama’a ga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

2027: INEC ta mayar da sunan Pantami, an hango abin da hakan zai jawo ga mutanen Gombe

Magoya bayan El-Rufai sun yi magana

Baba ta bayyana cewa magoya bayan El-Rufai sun himmatu wajen ci gaba da manufofin da tsohon gwamnan ya gada, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da kuma tallafa wa jama’a domin dogaro da kai.

Ta ce suna ganin ya kamata a ci gaba da ayyukan da suka shafi waɗannan fannoni domin inganta rayuwar al'ummar jihar.

ADC ta koka kan matsalar tsaro

Hafsat Baba ta kuma nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro da ke addabar wasu sassan jihar Kaduna, inda ta ambaci Birnin Gwari, Giwa da Millennium City a matsayin wuraren da lamarin ya fi tayar da hankali.

Ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar. Haka kuma, jigon ADC ɗin ta yi zargin cewa an kama sama da magoya bayan El-Rufai 30 kusan makonni biyu kafin gudanar da taron.

Ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin yawaitar kama mutanen da ke goyon bayan tsohon gwamnan, tare da tambayar dalilin da ya sa ake ci gaba da kama su.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya gano hanyar da Tinubu zai samu kuri'u cikin sauki a 2027

Baba ta buƙaci jami’an tsaro da su gudanar da ayyukansu ba tare da nuna son kai ba, tare da tabbatar da cewa suna bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya wajen gudanar da aikinsu.

El-Rufai ya bukaci a zabi ADC
Isa Ashiru Kudan tare da Nasir El-Rufai Hoto: Isa Ashiru Kudan
Source: Facebook

Uba Sani ya yi maganar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan magabacinsa, Malam Nasir Ahmad El-Rifai.

Gwamna Uba Sani ya ce bai taba fadin wani abu mara kyau game da Nasir El-Rufai ba, duk da rade-radin rashin kyakkyawar alaka da ake ganin ta shiga tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng