EFCC Ta Bankado Haramtacciyar Matatar Mai ta 'Yan Kasar Waje cikin Daji

EFCC Ta Bankado Haramtacciyar Matatar Mai ta 'Yan Kasar Waje cikin Daji

  • EFCC ta gano matatar mai ba bisa ƙa’ida ba a Ogere, Jihar Ogun, bayan gudanar da bincike da sa ido kan masu tace dattin mai
  • Binciken farko ya nuna cewa ana samo dattin man daga Warri da ke Delta, da Fatakwal a Jihar Rivers
  • EFCC ta ƙwace wurin, yayin da take binciken waɗanda ke gudanar da matatar, masu ita da kuma girman ayyukan da ake zargi da aikatawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ogun - Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ce ta gano wata matatar mai da ake gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba a yankin Ogere, Jihar Ogun, wadda ake zargin wasu ’yan China ne ke sarrafawa.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa jami’anta sun gano matatar ne a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, bayan tattara bayanan sirri da kuma sa ido kan ayyukan mutanen da ke tace dattin mai ba bisa ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

EFCC ta bankado matatar mai a Ogun
Matatar mai da ke aiki ba bisa ka'ida ba da EFCC ta gano Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamban 2026 a shafin X.

Yadda jami’an EFCC suka gano matatar

Oyewale ya ce jami’an hukumar na Lagos Zonal Directorate 2 ne suka kai samame wurin, amma sun tarar da shi babu kowa a lokacin da suka isa.

Ya bayyana cewa gano matatar ya biyo bayan wani samame da hukumar ta kai kan masana’antun sarrafa sinadarin lithium guda huɗu da ke yankin.

Duk da cewa babu wanda jami’an suka tarar a wurin, Oyewale ya ce sun gano ragowar kayayyakin da ake amfani da su wajen tace mai, da kuma wasu tankunan da aka binne a ƙarƙashin ƙasa.

A cewarsa, ana zargin an yi amfani da tankunan wajen dumama da sarrafa dattin mai da ake kira sludge oil.

Yadda ake sarrafa dattin man domin samar da dizal

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna da suka farmaki dakarun sojoji a Plateau

Mai magana da yawun EFCC ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ke gudanar da matatar suna samo dattin man ne daga Warri, Jihar Delta, da kuma Fatakwal, Jihar Rivers.Ya ce daga nan suke jigilar dattin man zuwa matatar da ke Ogere domin sarrafa shi.

Oyewale ya ƙara da cewa ana dumama dattin man da zafi mai tsanani, wanda ke sa wasu sinadaran mai masu sauƙin ficewa su ratsa ta cikin wasu ɗakuna da na’urorin tacewa.

A cewarsa, ana zargin wannan hanya ce ake amfani da ita wajen samar da dizal da ake shirin sayarwa a kasuwar Najeriya.

EFCC na binciken waɗanda ke da hannu

Oyewale ya ce wasu ma’aikatan da jami’an EFCC suka samu a wurin sun bayyana cewa masu gudanar da matatar ’yan China ne, amma ba su taɓa bayyana sunayensu ko sunan kamfanin da ke da alhakin gudanar da wurin ba.

Ya ce jami’an hukumar sun karɓi ragamar kula da wurin, yayin da suke ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda ke gudanar da ayyukan.

Haka kuma, binciken zai mayar da hankali kan gano masu mallakar matatar da kuma tantance cikakken girman ayyukan da ake zargin ana gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana kan sace dan takarar shugaban kasa, sun fadi abin da ya faru

EFCC ta ce tana gudanar da binciken ne domin gano dukkan waɗanda ke da hannu a lamarin da kuma tabbatar da ko an aikata zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa.

EFCC ta bankado matatar mai
Matatar man da EFCC ta bankado a Ogun Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Shugaban EFCC ya yabawa Gwamna Dauda

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede, ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal​ kan sauye-sauyen da ya ce ya gani a jihar Zamfara.

Shugaban EFCC ya lissafa sabon filin jirgin sama, titunan da aka shimfiɗa da kwalta da kuma sanya fitilu masu aiki da hasken rana a Gusau a matsayin wasu daga cikin alamomin ci gaban da aka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng