Mutanen Tinubu Sun Fita daga APC Sun Koma wajen Atiku a ADC

Mutanen Tinubu Sun Fita daga APC Sun Koma wajen Atiku a ADC

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi maraba da wasu magoya bayan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC
  • Atiku ya bayyana cewa waɗanda suka kafa gida suka fice daga cikinsa, ya kamata 'yan Najeriya su tambayi dalilin hakan, yana mai cewa sun gaji da yunwa da rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas
  • Ɗan takarar shugaban ƙasar na ADC ya ce yana fatan karɓar waɗanda suka sauya sheƙar a hukumance, tare da yin alƙawarin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da tsadar rayuwa idan suka samu nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi maraba da sauya sheƙar wasu magoya bayan Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima zuwa jam'iyyarsa.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Tinubu ya fada kan zabe bayan shiga dakin Ka'aba a Saudi

Atiku ya bayyana cewa ƙungiyar Northeast Strategic Engagement Initiative, wadda aka kafa domin yaƙin neman zaɓen Tinubu, Shettima da jam'iyyar APC, ta yanke shawarar komawa ADC.

Mutanen APC da suka koma ADC
'Yan APC da suka koma ADC tare da Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A cikin saƙon da ya wallafa a Facebook, Atiku ya ce yana fatan karɓar mambobin ƙungiyar a hukumance, yana mai bayyana sauya sheƙarsu a matsayin wani mataki na neman sabon salo na shugabanci.

Me Atiku ya ce kan sauya sheƙar?

Atiku ya bayyana cewa ya kamata 'yan Najeriya su yi tambaya kan dalilin da ya sa mutanen da suka taimaka wajen gina jam'iyyar APC da yaƙin neman zaɓen Tinubu suka yanke shawarar ficewa.

Ya ce waɗannan mutane sun ga irin matsalolin yunwa, rashin tsaro da rashin fata da gwamnatin Tinubu ta haifar wa al'ummar Arewa maso Gabas, shi ya sa suka zaɓi wata hanya ta daban.

A cikin saƙonsa, Atiku ya ce:

"Ina maraba da ƙungiyar Northeast Strategic Engagement Initiative, wadda aka kafa domin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu, Kashim Shettima da APC, zuwa jam'iyyar ADC. Ina fatan karɓar mambobinta a hukumance.
"Idan waɗanda suka gina gida suka fice daga cikinsa, ya kamata 'yan Najeriya su tambayi dalili. Sun ga yunwa, rashin tsaro da rashin fata da gwamnatin Bola ta jawo wa Arewa maso Gabas, kuma sun zaɓi wata hanya mafi kyau."

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince a sayawa sarakunan Abuja motocin alfarma

Atiku Abubakar a gidan shi
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

Alƙawuran da Atiku ya yi

Ɗan takarar shugaban ƙasar na ADC ya bayyana cewa haɗin gwiwarsu zai kawo ƙarshen matsalolin da ƙasar ke fuskanta idan suka samu damar jagorantar Najeriya.

Ya yi alƙawarin kawo ƙarshen rashin tsaro, rage tsadar rayuwa da samar da damarmakin ci gaba ga dukkan 'yan Najeriya.

Atiku ya kammala saƙonsa da cewa:

"Tare, za mu kawo ƙarshen rashin tsaro, rage tsadar rayuwa da buɗe damarmaki ga kowane ɗan Najeriya. Barka da dawowa gida."

Kwankwaso ya yi kira ga Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Dr Rabiu Kwankwaso, ya buƙaci Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027.

Kwankwaso ya yi wannan kira ne yayin da yake karɓar baƙuncin wasu 'yan siyasa da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja.

Tsohon gwamnan Kano ya yi nuni da shekarun Atiku da lafiyarsa, yana mai cewa ya kamata ya mayar da hankali kan nauyin sarautar gargajiya da yake riƙe da ita ta Wazirin Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng