Amsoshin Tambayoyin da 'Yan Najeriya Suka Fi Yi kan Tallafin N50,000

Amsoshin Tambayoyin da 'Yan Najeriya Suka Fi Yi kan Tallafin N50,000

Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda aka zaɓi waɗanda za su amfana da tallafin N50,000 na NERSI yayin amsa tambayoyi game da shirin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta fitar da cikakken bayani kan shirin tallafin NERSI, wanda aka ƙaddamar domin taimaka wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi wajen fuskantar tsadar rayuwa.

Bayanan sun ƙunshi yadda aka zaɓi waɗanda za su amfana, hanyoyin tantance cancanta, yadda za a karɓi N50,000 da kuma matakan kare kai daga masu damfara.

Moniepint da kudin Najeriya
Tambarin Moniepint da takardun kudin Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ga wasu muhimman tambayoyi da amsoshinsu kan shirin da kamfanij Moniepoint ya wallafa a shafinsa.

1. Menene shirin NERSI?

NERSI wani shiri ne na tallafin jinƙai da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar domin taimaka wa iyalai wajen rage raɗaɗin tsadar rayuwa. Ma'aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya ce ke gudanar da shirin.

Kara karanta wannan

Tallafin 50,000: Hanyoyi 6 da masu MoMo za su bi domin duba ko sun cancanta

2. Nawa za a ba mutum?

Kowane wanda aka zaɓa zai karɓi N50,000 a matsayin tallafi na lokaci ɗaya. Za a tura kuɗin gaba ɗaya zuwa asusun ajiyar kuɗi na wayarsa ba tare da cire wani kaso ba.

3. Shin tallafin rance ne?

A'a. Tallafi ne na kyauta daga gwamnatin tarayya, don haka babu buƙatar wanda ya karɓa ya mayar da kuɗin.

4. Shin za a ci gaba da biyan tallafin?

A'a, wannan tallafi na Naira 50,000 ne na lokaci ɗaya. Idan gwamnati ta yanke shawarar ƙarin tallafi, za ta sanar da hakan ta hanyoyin sadarwarta na hukuma.

5. Waye mai tura kudin?

Gwamnati ta amince da kamfanonin hada-hadar kuɗi na zamani da za su taimaka wajen biyan tallafin, ciki har da:

  • ALAT by Wema
  • MoMo PSB
  • NairaGram
  • OPay
  • Moniepoint

6. Shin tallafin ya takaita ga wasu?

A'a. Ana zaɓar waɗanda za su amfana daga dukkan yankunan ƙasar guda shida bisa buƙatarsu, ba tare da la'akari da addini, ƙabila ko jam'iyyar siyasa ba.

Kara karanta wannan

Yadda masu amfani da MTN za su samu tallafin N50,000

Ana gudanar da biyan tallafin ne a matakai daban-daban, saboda haka wasu za su iya samun saƙon sanarwa kafin wasu.

7. Shin akwai kuɗin rajista?

A'a. Rajista, karɓar tallafin da amsa saƙonnin shirin duk kyauta ne. Ba a buƙatar mutum ya biya wani kuɗi domin karɓar N50,000.

Sai dai idan mutum ya je cire kuɗinsa ta hannun wakilin POS, yana iya biyan kuɗin cire kuɗi na yau da kullum.

8. Ta yaya za a zabi mutane?

An zaɓi waɗanda za su amfana ne daga rajistar tallafin jinƙai ta ƙasa da kuma bayanan katin shaida na ƙasa da aka tantance.

An samo lambobin wayoyinsu ne daga waɗannan bayanai na hukuma.

9. Za a kiyaye bayanan sirri?

Eh. Gwamnati ta ce tana kare bayanan mutane bisa dokar kare bayanan sirri ta Najeriya ta 2023. Ana raba bayanan ne kawai da kamfanin da aka ware wa mutum domin biyan tallafinsa.

Wakilan gwamnati ba za su nemi lambar sirrin asusu (PIN), lambar tabbatar da ciniki (OTP) ko BVN na mutum ba.

10. Ta yaya zan yi rajistar tallafin?

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: Gwamnatin Tarayya ta fitar da ka'idoji 4, ta ja kunnen 'yan Najeriya

Babu buƙatar cike fom ko yin wata rajista. Ana zaɓar waɗanda za su amfana ne kai tsaye daga bayanan rajistar tallafin jinƙai ta ƙasa da kuma bayanan katin shaida da aka tantance.

Babu wani wakili ko mutum na daban da zai iya saka sunan wani cikin jerin waɗanda za su amfana.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na yi wa jama'a bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

11. Ta yaya zan gano ko an zaɓe ni?

Za ka iya amfani da wayar hannu domin duba cancantarka ta hanyar buga lambar kamfanin da aka ware maka.

Ga lambobin kamfanonin:

  • ALAT by Wema: *945*23#
  • MoMo PSB: *671*0#
  • NairaGram: *726*00#
  • Moniepoint: *5573*27#
  • OPay: *955*20#

Bayan ka buga lambar da ta dace, zaɓi tantance cancanta, sannan ka bi umarnin da zai bayyana.

12. Ta yaya zan san cewa an zaɓe ni?

Za ka samu saƙon waya daga kamfanin da aka ware maka domin biyan tallafin. Saƙon zai ƙunshi umarnin da za ka bi da lambar da za ka buga domin amincewa da karɓar kuɗin.

13.Me ya sa ban samu ba sakon ba?

Ana biyan tallafin ne a matakai daban-daban a faɗin ƙasar. Saboda haka, rashin samun saƙo a yanzu ba yana nufin ba za ka iya samun saƙon a wani mataki na gaba ba.

Kara karanta wannan

Yadda Opay, Moniepoint ke tantance lambobi don samun tallafin N50,000

Haka kuma, ba dukkan mutanen da ke wani yanki ne za a zaɓa a lokaci guda ba.

14. Wani zai iya taimaka min?

A'a. Ana zaɓar waɗanda za su amfana ne ta hanyar tsarin bayanan hukuma. Duk wanda ya ce zai iya saka sunanka ko hanzarta biyan kuɗinka, musamman idan ya nemi kuɗi, yana iya ƙoƙarin damfararka.

15. Ta yaya za samu kudin bayan SMS?

Buga lambar da aka turo maka ta amfani da lambar wayar da ta karɓi saƙon. Bi umarnin da zai bayyana, sannan ka zaɓi amincewa da karɓar tallafin.

Bayan ka amince, za a buɗe maka asusun ajiyar kuɗi na wayar salula, sannan a saka maka N50,000. Za ka kuma samu saƙon tabbatar da an tura kuɗin.

16. Dole sai ina da babbar waya?

A'a. Za ka iya amfani da lambobin USSD a waya ta yau da kullum ba tare da amfani da intanet ko sayen data ba.

17. Ya zan yi idan na goge saƙon tallafin?

Ba sai ka nemi saƙon farko ba. Za ka iya sake buga lambar kamfanin da aka ware maka, sannan ka zaɓi tantance cancanta domin ci gaba da karɓar tallafin.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: Yadda ake duba cancanta da karbar kudin cikin sauki

18. Me zai faru idan na zaɓi amsar A'a?

Idan ka zaɓi A'a lokacin da aka tambaye ka kana son karɓar tallafin, za a dakatar da biyan kuɗin. Idan ka sauya ra'ayi ko ka zaɓi A'a bisa kuskure, za ka iya sake buga lambar kamfanin, sannan ka zaɓi E domin amincewa da karɓar tallafin.

19. Ta yaya zan cire kuɗin?

Akwai hanyoyi daban-daban da za ka iya amfani da su:

  • Wakilin POS: Za ka iya tura kuɗin daga asusunka zuwa ga wakilin POS, sannan ya ba ka kuɗin hannu.
  • Asusun banki: Za ka iya tura kuɗin kai tsaye zuwa asusun bankinka ta lambar USSD ko manhajar kamfanin.
  • Ofisoshin kamfani: Masu amfani da ALAT za su iya amfani da rassan Wema Bank, yayin da masu MoMo da NairaGram za su iya amfani da wakilansu.

20. Zan iya amfani da sashen kudin?

Eh. Za ka iya cire dukkan kuɗin ko wani kaso daga ciki. Duk kuɗin da ka bari zai ci gaba da kasancewa a asusunka na wayar salula.

Kara karanta wannan

Moniepoint ya fitar da hanya mai sauki ta duba waɗanda za su samu tallafin N50,000

21. Wani zai iya karɓar kuɗin a madadina?

A'a. An haɗa tallafin da takamaiman lambar waya da asusun wanda aka zaɓa. Wani na kusa da kai zai iya taimaka maka wajen buga lambar, amma kai ne ya kamata ka shigar da PIN ɗinka.

Kada ka ba wani PIN, OTP ko wayarka domin karɓar tallafin a madadinka.

22. Ya zan kubuta daga 'yan damfara?

Kada ka bayyana PIN, OTP, BVN ko kalmar sirrin asusunka ga kowa, ciki har da ma'aikatan kamfanonin biyan kuɗi ko jami'an gwamnati.

Haka kuma, kada ka biya wani kuɗi domin a buɗe maka asusu, a saka sunanka cikin jerin waɗanda za su amfana ko a saki tallafinka.

Ka guji danna hanyoyin yanar gizo da ba ka sani ba ko sauke manhajojin da aka turo maka ta saƙon waya ko WhatsApp da sunan NERSI. Shirin ba ya amfani da irin waɗannan hanyoyin domin tantance cancanta.

23. Me zan yi idan na zargi wani?

Idan ka bayyana PIN ko OTP ɗinka ga wani, ko ka lura da wani ciniki da ba ka amince da shi ba, ka tuntubi kamfanin da ke kula da asusunka nan take.

Kara karanta wannan

Opay, Moniepoint da bankuna 5 da ke tura tallafin N50,000 a Najeriya

Ka nemi a kulle asusun ko a sauya bayanan sirrinka domin hana wani amfani da kuɗinka ba tare da izininka ba.

Opay ya fara tura kudin

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta fara biyan tallafin N50,000 ga wasu 'yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.

Shirin na tallafa wa iyalai matalauta da masu rauni a faɗin ƙasar ta hannun kamfanonin hada-hadar kuɗi na zamani da gwamnati ta amince da su.

Bayanin da OPay ya fitar ya nuna cewa masu amfani da kamfanin za su iya tantance cancantarsu ta hanyar buga *955*20# da lambar wayar da suka haɗa da asusunsu, ba tare da biyan kuɗin rajista ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng