Kungiyar Amnesty Ta Shiga Batun Kisan Sheikh Masussuka a Katsina

Kungiyar Amnesty Ta Shiga Batun Kisan Sheikh Masussuka a Katsina

  • Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan Sheikh Yahaya Masussuka, wanda ’yan bindiga suka harbe
  • Kungiyar ta bukaci hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a kisan a gaban shari’a
  • Marigayin ya shahara wajen wa’azin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, duk da cewa ya taba fuskantar barazana da takaddama kan wasu koyarwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka.

Wasu ’yan bindiga ne dai suka kashe Sheikh Masussuka a karamar hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina.

Amnesty ta yi magana kan kisan Masussuka
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka Hoto: Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka
Source: Facebook

A cikin sanarwar da ta fitar a shafin X ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026, kungiyar ta bukaci hukumomin Najeriya su gudanar da bincike cikin gaggawa da inganci domin gano wadanda suka aikata laifin tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban shari’a.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina ya fadi matakin da za a dauka kan kashe Masussuka

Yadda ’yan bindiga suka kashe Masussuka

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren Litinin a kofar gidan malamin da ke garin Dutsin-Ma.

An ruwaito cewa ’yan bindigar, wadanda ke kan babura, sun bude wuta kan wasu mutane biyu a lokacin da Sheikh Yahaya Masussuka ke shirin fita daga gidansa domin gudanar da wa’azin da ya saba yi da yamma.

An garzaya da wadanda aka harba zuwa asibitin Dutsin-Ma domin ba su kulawar gaggawa, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsu.

Har yanzu, bayanan da aka bayar ba su fayyace cikakken dalilin harin ko wadanda ake zargi da aikata shi ba.

Gudummawar malamin wajen zaman lafiya

Amnesty International ta bayyana cewa Sheikh Yahaya Masussuka ya shahara wajen amfani da wa’azinsa wajen karfafa hadin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar Musulmi.

Ta ce malamin ya kuma kasance mai kira ga tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban, tare da yin wa’azi kan illolin tsattsauran ra’ayi da shiga harkokin masu tsattsauran ra’ayin addini.

Kara karanta wannan

InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un, an kashe Sheikh Yahaya Masussuka a ƙofar gidansa

Sai dai kungiyar ta bayyana cewa marigayin ya shafe tsawon rayuwarsa yana fuskantar barazana da tsoratarwa.

Amnesty ta jaddada cewa dole ne hukumomi su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da adalci ga wadanda aka kashe tare da kare rayukan sauran al’umma.

Ya taba fuskantar takaddama kan wa’azinsa

Sheikh Yahaya Masussuka ya taba shiga takaddama kan wasu daga cikin koyarwarsa ta addini.

A ranar 18 ga Nuwamba, 2025, gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da cewa za a bukaci malamin ya kare wa’azinsa a gaban wani kwamiti da ya kunshi malaman addinin Musulunci.

Sai dai babu wata alama da ke tabbatar da cewa takaddamar da ta gabata tana da alaka da kisan da aka yi masa a daren Litinin.

An kashe Masussuka a Katsina
Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka da aka kashe a Katsina Hoto: Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka
Source: Facebook

Sheikh Maqari ya yi magana kan kisan Masussuka

A wani labarin kuma, kun ji cewa limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari, ya yi Allah wadai da kisan malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a jihar Katsina.

Farfesa Maqari ya bayyana damuwarsa kan kisan, yana mai cewa abin da ya faru na iya zama makomar duk wanda yake son bayyana abin da ya yi imani da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng