Kotu Ta Yanke Wa Mutum 2 Hukunci kan Kisan Surukin Gwamna a Najeriya

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 2 Hukunci kan Kisan Surukin Gwamna a Najeriya

  • Babbar Kotun Jihar Bayelsa da ke Yenagoa ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe mutane uku a 2022
  • Daya daga cikin wadanda aka kashe, Odeinyefa Ogbolosingha, surukin Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ne
  • An samu Gideon Atama da Clever Ovo da laifin hada baki, garkuwa da mutane, kisan kai da yunkurin kisan kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau dakullum

Bayelsa, Nigeria - Babbar Kotun Jihar Bayelsa da ke Yenagoa ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe mutane uku.

Daga cikin wadanda mutanen biyu suka kashe har da Odeinyefa Ogbolosingha, wanda surukin Gwamna Douye Diri ne, a garin Kalaba da ke Karamar Hukumar Yenagoa a watan Yuni na 2022.

Gwamna Diri.
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri a fadar gwamnatinsa da ke Yenagoa Hoto: Douye Diri
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa sauran wadanda aka kashe su ne Sarkin Kalaba, HRH Kolibo Francis Amabelimo, da kuma Samuel Oburo.

Kara karanta wannan

'Sai mai tsoron Ubangiji': Gwamna ya ba da satar amsa ga magajinsa a zaɓen 2028

Kotun ta yanke masu hukunci

Wadanda aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya su ne, Gideon Atama, mai shekaru 32, da Clever Ovo, mai shekaru 33.

An gurfanar da mutanen bisa zargin hada baki, garkuwa da mutane, kisan kai da kuma yunkurin kisan kai, a karar mai lamba BYHC/YHC/CR/32/2025.

A hukuncin da ya yanke a ranar Talata, Alkalin kotun, Mai Shari’a Michael Amadise Ekade, ya samu wadanda ake tuhumar biyu da laifi bayan nazarin hujjojin da aka gabatar a gaban kotu, inda ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mutuwar wani wanda ake tuhuma

Shari’ar ta fuskanci tsaiko bayan mutuwar wani mutum da ake tuhuma tare da su, Bethlehem Nwanlia, mai shekaru 50, wanda rahotanni suka ce ya fadi kasa ya mutu a harabar Babbar Kotun Jihar Bayelsa a ranar 27 ga Oktoba, 2026.

An ce Nwanlia ya samu matsalolin lafiya, ciki har da hawan jini da shanyewar jiki, a lokacin da yake tsare a gidan gyaran hali da ke Okaka.

Kara karanta wannan

Mutane 17 da ƴan bindiga suka sace a wurin ibada sun rasa rayukansu

Mutuwarsa ta rage yawan wadanda ake tuhuma a shari’ar da kotun ta yanke wa sauran hukunci.

An fara gurfanar da wadanda ake tuhumar ne bayan binciken da ’yan sanda suka gudanar kan kisan mutanen uku, wanda ya kai ga kama wadanda ake zargi da kuma gurfanar da su a gaban Babbar Kotun jihar.

Iyalan mamatan sun yaba

Wasu daga cikin ’yan uwan mamatan sun nuna godiyarsu ga jami’an ’yan sandan da ke sashen VCRU, musamman tawagar da CSP Nwaogbo ke jagoranta, bisa kamawa da binciken da suka gudanar wanda ya kai ga samun hukuncin da kotu ta yanke.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a kotuna a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sun kuma yaba wa gwamnatin Jihar Bayelsa, ta hannun Ma’aikatar Shari’a, kan abin da suka bayyana a matsayin gurfanar da shari’ar cikin kwarewa da himma.

Iyalan sun ce hukuncin yana da matukar muhimmanci a gare su, domin yana wakiltar wani mataki na samun adalci ga ’yan uwansu da suka rasa rayukansu a harin da aka kai a shekarar 2022.

Kotu ta yanke wa yan JTF hukuncin kisa

Kara karanta wannan

Da gaske an ɗaure mace kirista saboda ta sa musulmi ya yi ridda? An samu bayani

Kun ji cewa Babbar Kotun Jihar Sokoto ta yanke wa wasu mambobi uku na rundunar sa-kai ta Civilian Joint Task Force (CJTF) hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun ta umarci a rataye jami'an tsaron ne bayan ta same su da laifuffukan haɗa baki domin aikata laifi, fashi da makami da kuma kisan kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262