Bayan Kama Su da Laifi, Za a Rataye Jami'an Tsaro 4 Har Lahira a Arewacin Najeriya
- An yanke wa wasu jami'an tsaro uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin fashi da makami da kisan kai
- An zarge su da kwace N260,000 daga hannun Babangida Nasiru kafin daga baya a gano gawarsa da raunukan harbin bindiga
- Mai shari’a Kabiru Muhammad ya ce waɗanda aka yanke wa hukuncin na da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 90
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Wata Babbar Kotun Jihar Sokoto ta yanke wa wasu mambobi uku na rundunar sa-kai ta Civilian Joint Task Force (CJTF) hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama su da laifi.
Kotun ta umarci a rataye jami'an tsaron ne bayan ta same su da laifuffukan haɗa baki domin aikata laifi, fashi da makami da kuma kisan kai.

Source: Getty Images
Waɗanda aka yanke wa hukuncin su ne Gaji Hassan, Abdullahi Goni Gudusu da Modu Bukar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Tirkashi: An yanke wa mutumin da ya kashe abokinsa kan tashi sallar Asubah hukunci a Kano
A hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, 2026, a shari’ar mai lamba SS/78C/2026, Mai shari’a Kabiru Muhammad ya same su da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume uku da ake yi musu.
Yadda lamarin ya faru
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kotun, Nakwanta Muhammad Garba, ya fitar, lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Satumba, 2024, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a ƙauyen Kagara, da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
Kotun ta ji cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin, waɗanda ke ɗauke da bindigogi, sun tare wani mutum mai suna Babangida Nasiru da wata mata da ke tare da shi, kafin su tafi da su cikin daji.
Rahoton ya bayyana cewa sun karɓi kuɗi N260,000 daga hannun Nasiru sannan suka ci gaba da riƙe shi a hannunsu. Daga baya, an gano gawarsa da raunukan harbin bindiga a ƙirjinsa da wuyansa.
Shaidu sun tabbatar da laifinsu
A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu biyu a gaban kotun. Mai shari’a Muhammad ya bayyana shaidar wanda ya tsira daga lamarin kuma ya ga abin da ya faru da idanunsa a matsayin sahihiya.
Kotun ta ƙi amincewa da ikirarin waɗanda ake tuhuma na cewa sun saki marigayin. Mai shari’ar ya ce sun gaza bayyana yadda mutumin ya mutu, bisa ƙa’idar shari’a da aka sani ta ganin karshe.
Haka kuma, Mai shari’a Muhammad ya yanke hukuncin cewa amsa da laifin da waɗanda ake tuhuma suka yi tun farko zai iya zama hujja.

Source: Original
An ba su damar ɗaukaka ƙara
Bisa tanadin hukuncin da ya wajaba a ƙarƙashin dokar laifuffuka ta Jihar Sokoto ta shekarar 2019, kotun ta yanke wa kowanne daga cikin mutanen uku hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Sai dai, Mai shari’a Muhammad ya sanar da su cewa suna da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara cikin kwanaki 90.

Kara karanta wannan
Mutuwar uwa, fadan ‘ya ‘yansa da abubuwa 10 da suka faru da El Rufai da yake tsare
Kotu ta hukunta masu garkuwa a Edo
Kun ji cewa kotu ta musamman ta Jihar Edo da ke zama a Benin City, ta gamsu da hujjojin da aka gabatar mata, ga kama wasu mutum hudu da hannu a garkuwa da mutane.
Sakamakom haka, babbar kotun ta yanke wa mutanen huɗu da aka samu da laifi hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Asali: Legit.ng
