"Zan Samar da Irin Dangote 20 a Shekara 4"; Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fadi Shirinsa
- Adewole Adebayo ya ce gwamnatinsa za ta samar da attajirai irin Aliko Dangote 20 cikin shekaru huɗu
- Ya yi alƙawarin bai wa matatun mai rangwamen haraji na dogon lokaci da kuma tabbacin dokoki domin ƙarfafa jarin masu zaman kansu
- Adebayo ya ce za a ba matatun mai kwanaki 90 su biya kuɗin ɗanyen man da gwamnati ta samar musu bayan sun tace shi sun sayar a ƙasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027, gwamnatinsa za ta samar da attajirai irin Aliko Dangote guda 20 cikin shekaru huɗu.
Adebayo ya ce zai cimma hakan ne ta hanyar tallafa wa matatun mai da ƙarfafa fitar da kayayyakin da ake sarrafawa a Najeriya zuwa ƙasashen waje.

Kara karanta wannan
An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Source: Twitter
Ya bayyana wannan alƙawari ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Road to 2027 na gidan rediyon Nigeria Info,
Dan takarar ya yi bayani kan yadda zai rage farashin man fetur ba tare da lalata jarin masu zaman kansu a harkar matatun mai ba.
Yadda zai samar da attajirai irin Dangote 20
Adebayo ya ce gwamnatinsa za ta samar da manyan ’yan kasuwa masu ƙarfin tattalin arziki ta hanyar ƙarfafa masana’antun tace mai da za su fitar da kayayyakinsu zuwa ƙasashen waje.
A cewarsa, Najeriya na da damar da za ta yi amfani da ita wajen samun kuɗaɗen ƙasashen waje ta hanyar tace ɗanyen mai da sayar da shi a kasuwannin duniya.
“Gwamnatinmu za ta samar da attajirai irin Dangote guda 20 cikin shekaru huɗu domin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje. Wannan ne ya sa Allah ya ba Najeriya matatar mai a bakin ruwa.” In ji shi.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Mai garkuwa da mutane ya shiga hannu yana kokarin karbar kudin fansa
Dan takarar ya bayyana cewa zai bai wa matatun mai rangwamen haraji na dogon lokaci tare da tabbatar da cewa dokokin da ke jagorantar harkokin kasuwancinsu ba za su riƙa sauyawa ba tare da dalili ba.
Zai bai wa matatun mai kwanaki 90
Adebayo ya ce gwamnatinsa za ta bai wa matatun mai damar karɓar ɗanyen man da gwamnati ta samar, sannan su samu kwanaki 90 kafin biyan kuɗinsa.
Ya bayyana cewa hakan zai ba su damar tace ɗanyen man, jigilar kayayyakin zuwa ƙasashen waje, karɓar kuɗin daloli kafin su biya gwamnatin Najeriya.
“Idan na sayar maka da ɗanyen mai, zan ba ka kwanaki 90 ka biya. Wannan ya ninka yawan man da za ka iya tacewa sau biyu. Za ka tace man, ka aika da shi ƙasashen waje, ka karɓi daloli, sannan ka biya ni.” In ji shi.
Ya ce wannan tsari zai taimaka wajen rage matsin kuɗi da ke kan masu gudanar da matatun mai, tare da ƙarfafa musu gwiwar zuba jari a harkar.

Source: Facebook
Adewole ya yi gargadi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Adewole Adebayo, ya yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na soke gangamin siyasa ko sauya lokacin zaɓen 2027 saboda barkewar cutar Ebola.
A cewarsa, bai kamata a soke gangamin siyasa, tarukan yaƙin neman zaɓe ko kuma a sauya babban zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng