Wani Faifan Bidiyo na Neman Jefa Dan Majalisar Kano a Gagarumar Matsala
- Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tura batun Hon. Yusuf Bello Aliyu zuwa kwamitin da'a da gata domin bincike kan wani bidiyo a kafafen sada zumunta
- Ana zargin dan majalisar mai wakiltar Nasarawa da yi wa Gwamna Abba Yusuf shagube, wanda hakan ya ja hankalin Majalisa
- Wasu 'yan majalisar sun bukaci a binciki lamarin tare da daukar matakin ladabtarwa idan an tabbatar da zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - An shiga fargaba a Majalisar Dokokin Jihar Kano a zaman ranar Talata, yayin da 'yan majalisa suka dauki matakin bincikar wani abokin aikinsu, Yusuf Bello Aliyu, mai wakiltar mazabar Nasarawa.
Majalisar Kano za ta binciki mambanta ne kan zargin wallafa wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ake cewa ya yi wa Gwamna Abba Yusuf shagube.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: Dalilin da ya sa 'yan majalisa 8 suka je wurin Tinubu bayan sun fice daga APC

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa Majalisar ta mika batun ga Kwamitin Da'a da Gata domin gudanar da bincike, bayan dan majalisa mai wakiltar Minjibir, Abdulhamid Abdul, ya gabatar da batun gaggawa.
Laifin da ake zargin dan Majalisa
Abdul ya ce ya damu matuka da wani bidiyo da ya wallafa, wanda ake zargin ya nuna dan majalisar da ake zargi yana rike kunnuwan zomo tare da furta kalaman da aka dauka a matsayin rashin girmamawa ga gwamnan.
Ya bukaci majalisar da ta binciki yadda lamarin ya faru tare da daukar matakin ladabtarwa da ya dace idan bincike ya tabbatar da zargin.
A cewarsa, wajibi ne 'yan majalisa su kare mutuncin mukamansu tare da guje wa duk wani hali da zai iya rage amincewar jama'a da majalisar.
Ya kuma bukaci a nemi dan majalisar ya ba da hakuri a bainar jama'a tare da yi masa gargadi ko daukar matakin ladabtarwa da ya dace idan bincike ya same shi da laifi.
An goyi bayan majalisa ta yi bincike
Da yake goyon bayan kudirin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Takai, Musa Kachako, ya ce lamarin ya nuna bukatar 'yan majalisa su magance abin da ya bayyana a matsayin karuwar amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ba ta dace ba.
Ya bukaci majalisar ta yi la'akari da kafa dokar da za ta magance wallafa sakonnin cin zarafi a intanet, yana mai cewa ya kamata zababbun wakilai su nuna halin dattako da kulawa a sakonnin da suke wallafawa ga jama'a.

Source: Facebook
Shi ma dan majalisa mai wakiltar Madobi, Sulaiman Mukhtar, ya goyi bayan kudirin, yana mai cewa bambancin ra'ayin siyasa bai kamata ya zama dalilin rashin girmamawa ba.
A karshen tattaunawar, Kakakin Majalisa ya mika batun ga Kwamitin Da'a da Gata tare da umartar sa da ya dawo da rahotonsa gaban majalisar a ranar Laraba.
Majalisa ta dakatar da ciyamomi 3 a Kano
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Bebeji, Rogo da Bagwai na tsawon watanni uku.
Kakakin majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya ce an ɗauki matakin ne domin bai wa kwamitin bincike damar gudanar da aikinsa cikin adalci.
Majalisar ta ce shugabannin na iya rasa kujerunsu idan bincike ya tabbatar da zarge-zargen da ake yi musu wanda ya shafi almundahanar kudi.
Asali: Legit.ng

