Babbar Magana: Sarki a Najeriya Ya Shigar da Gwamna Kara Kotu

Babbar Magana: Sarki a Najeriya Ya Shigar da Gwamna Kara Kotu

  • Apetumodu na Ipetumodu a jihar Osun, Oba Joseph Oloyede, ya maka Gwamna Ademola Adeleke a kotu kan shirin maye gurbinsa
  • Oba Oloyede ya nemi kotu ta hana gwamnan da jami'ansa naɗa wani sabon basarake har sai an kammala sauraron ƙarar da ya shigar
  • Matakin ya biyo bayan tsige tsohon sarkin daga sarautarsa sakamakon tabbatar da laifinsa a Amurka kan zargin damfarar haraji da safarar kuɗin haram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun – Tsohon Apetumodu na Ipetumodu a jihar Osun, Oba Joseph Oloyede, ya maka Gwamna Ademola Adeleke a kotu, inda yake neman a hana gwamnatin jihar naɗa wanda zai maye gurbinsa.

Oba Oloyede, wanda aka kama shi da laifi a Amurka kan damfarar haraji da safarar kuɗin haram, ya ce gwamnan bai sanar da shi a hukumance laifin da ya aikata ba kafin fara shirin maye gurbinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya yi ta'aziyyar shugaban karamar hukumar da ya rasu a Bauchi

Oba Joseph Oloyede da Gwamna Ademola Adeleke
Gwamna Ademola Adeleke da Oba Joseph Oloyede. Hoto: Osun State Government
Source: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa tsohon basaraken ya shigar da ƙarar ne a babbar kotun jihar Osun da ke Ile-Ife, inda ya nemi a dakatar da duk wani mataki na naɗa sabon Apetumodu har sai an kammala shari'ar.

Abin da sarkin ke nema a kotu

Oba Oloyede, wanda shi ne mai ƙara na biyu a shari'ar mai lamba HIF/50/2026, ya shigar da buƙatarsa a gaban kotu ta hanyar takardar neman umarnin wucin gadi.

A cikin takardar mai ɗauke da ranar 16 ga Satumba, 2026, ya nemi kotu ta hana gwamna ko wani jami'in gwamnatinsa ɗaukar matakin cike sarautar Apetumodu ko naɗa wani mutum a madadinsa.

Ya bayyana cewa ba a taɓa sanar da shi wani laifi da ya aikata ba kafin sanar da tsige shi daga sarautar.

A cikin takardar, ya ce:

"A cikin jaridar The Guardian ta ranar 11 ga Mayu, 2026, an yi zargin cewa gwamna ya sanya hannu kan wata takardar tsige mai ƙara na biyu daga sarautar Apetumodu a ranar 7 ga Mayu, 2026, ba tare da wani sahihin dalili na doka ba."

Kara karanta wannan

Tambuwal ya fusata da aka kai wa dan takarar ADC hari da bindiga a Sokoto

Ya kuma yi zargin cewa gwamnan da wasu jami'an gwamnati ba su sanar da shi wani laifi da ya aikata ba kafin fitar da sanarwar tsige shi.

Waɗanda aka shigar da ƙarar

Baya ga Gwamna Ademola Adeleke, sauran waɗanda aka shigar da su cikin ƙarar sun haɗa da babban lauyan gwamnatin jihar Osun kuma kwamishinan shari'a, da kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin sarautun gargajiya.

Haka kuma, ƙarar ta shafi Chief Afolabi Adedeji, Asalu na Ipetumodu kuma shugaban masu zaɓen sarki, Chief Adesoye Babalola, Malefon na Ipetumodu da ƙaramar hukumar Ife ta Arewa.

Sauran masu ƙarar sun haɗa da Prince Oyewusi Adewusi, Prince Isaac Adewuni da Prince Abiodun Oyetoro, waɗanda suka shigar da ƙarar a madadinsu da sauran 'yan gidan sarautar Latimogun na gidan Aribile da ke Ipetumodu.

Taswirar jihar Osun
Taswirar jihar Osun a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Alƙali Dapo Adeniji ya amince da buƙatar, inda ya ɗage shari'ar zuwa ranar 21 ga Janairu, 2027, tare da umartar a sake fitar da sanarwar zaman kotu a miƙa wa waɗanda ake ƙara.

Adeleke yi magana kan APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Ademola Adeleke ya musanta cewa ya yi yarjejeniya da APC kan rabon kujerun takara.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka kafa gwamnatinsu, suke karɓar haraji kala 3 a jihohin Arewa 2

Rahoto ya nuna cewa gwamnan ya ce haɗin gwiwarsa da fadar shugaban ƙasa na da alaƙa ne kawai da sake zaɓen Bola Tinubu a 2027.

A bayanin da ya yi, ya tabbatar da cewa zai goyi bayan ’yan takarar jam’iyyar Accord a zaɓen majalisar dattawa, wakilai da majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng