'Yan Bindiga Sun Tafka Barna da Suka Farmaki Dakarun Sojoji a Plateau
- 'Yan bindiga sun kai hari kan dakarun Operation Enduring Peace a shingen binciken Sopp da ke Ungwan Boka,
- Maharan sun tsere bayan musayar wuta da sojoji, amma sun yi awon gaba da makamai biyu na jami'an tsaron
- Harin ya zama na uku cikin mako guda da aka kai wa jami’an sojoji a Plataeua, bayan wasu hare-hare biyu a Mangu da Jos ta Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan dakarun Operation Enduring Peace (OPEP) a wani shingen binciken ababen hawa da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato, inda suka kashe soja guda ɗaya tare da yin awon gaba da makamai biyu.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoban 2026 lokacin da wasu dakarun rundunar Sector 6 ta OPEP da aka girke a Ungwan Boka suka fuskanci harin a shingen Sopp.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya ruwaito cewa maharan sun buɗe wa sojojin wuta daga wurare daban-daban, lamarin da ya jawo musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.
Bayan musayar wutar, maharan sun tsere zuwa cikin dazuzzukan da ke kewaye da yankin.
An kashe soja yayin musayar wuta
Majiyoyi sun bayyana cewa yayin artabun, maharan sun kashe wani soja sajan da ke aiki a cibiyar kula da lafiyar dakarun Najeriya da ke Tigi.
A cewar majiyoyin, sojan ya je wurin ne domin gudanar da wani aikin ofis lokacin da maharan suka kai farmakin.
Daga bisani, an dauki gawarsa zuwa ɗakin ajiyar gawawwaki na asibitin rundunar sojoji ta 3 Division Medical Services and Hospital (3 DMSH).
Rahotanni sun kuma bayyana cewa dakarun agaji sun fara gudanar da samame domin bin sawun maharan da suka tsere, tare da ƙoƙarin gano makaman da suka sace.
An kai hare-hare 3 kan sojoji cikin mako guda
Wannan sabon harin ya zama na uku cikin mako guda da aka kai wa jami’an sojojin Najeriya a jihar Plateau.
A ranar 29 ga Oktoba, wasu matasa da ake zargin ’yan yankin ne sun kai hari kan jami’an tsaro yayin wani zanga-zanga a kan hanyar Jos zuwa Mararaban Pushit da Pankshin, a ƙaramar hukumar Mangu.
Masu zanga-zangar sun fito ne domin neman a saki wani mutum mai suna Karfe, wanda ake zargin mamba ne a ƙungiyar mayaƙan kabilar Mwaghavul.
An kama Karfe ne bisa zargin hannu a kisan wani dattijon Fulani a kan hanyar Jipun zuwa Jennaret.
An farmaki wani soja a Jos ta Kudu
Haka kuma, a ranar 29 ga Oktoba, wasu mutanen yankin da ake zargi sun farmaki wani sojan Najeriya mai suna Gbonogbe Mensewon, wanda ke matsayin Laftanar Kofur, a Bukuru, ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sari sojan da adda a ƙirji, ciki da kansa, yayin da wasu fararen hula biyu suka samu raunukan harbin bindiga.
An garzaya da sojan zuwa asibitin ECWA da ke Bukuru, inda aka ba shi kulawar gaggawa har aka tabbatar da daidaituwar lafiyarsa. Daga bisani, aka tura shi zuwa asibitin Bingham da ke Jos domin ci gaba da jinya.

Source: Original
'Yan ta'adda sun kashe dan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan ta’addan Mamudawa/Lakurawa ne sun kashe sufeton ’yan sanda da fararen hula 11 a hare-haren da suka kai ƙauyukan Waiwayi da Kystu, da ke ƙaramar hukumar Koko/Besse a jihar Kebbi.
Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutanen, inda ta bayyana cewa sufeton ya rasu ne yayin musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan.
Asali: Legit.ng


