Tinubu Ya Yaba wa Sarkin Musulmi a Bikin Cika Shekara 20 a Mulki

Tinubu Ya Yaba wa Sarkin Musulmi a Bikin Cika Shekara 20 a Mulki

  • Shugaba Bola Tinubu ya taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 yana kan karagar mulki
  • Tinubu ya yabawa Sarkin Musulmin kan rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kan addinai da ci gaban Najeriya
  • Shugaban kasar ya yi masa addu’ar samun lafiya, tsawon rai da karin hikima domin ci gaba da jagorantar al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulki.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna da ya aika wa Sarkin Musulmin, inda ya yaba da yadda ya jagoranci masarautar cikin shekarun da suka gabata.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya cika shekara 20 a kan karagar mulki

Sultan da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Sarkin Musulmi. Hoto: Bayo Onanuga|JNI
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, shugaban kasar ya ce Sarkin Musulmin ya yi amfani da sarautarsa wajen karfafa zaman lafiya, hadin kan kasa da ci gaban al’umma.

Tinubu ya yabawa Sarkin Musulmi

A sakon nasa, Tinubu ya ce shekaru 20 da suka gabata, Sarkin Musulmin ya hau karagar mulki cikin tawali’u, jarumta da fahimtar nauyin da ke kansa.

Ya bayyana cewa a tsawon wannan lokaci, Sarkin Musulmin ya kiyaye kyawawan al'adun Daular Usmaniyya tare da habaka martabarta da amfani da ita wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Shugaban kasar ya kuma bayyana Sarkin Musulmin a matsayin shugaba mai hikima, natsuwa a lokutan tashin hankali da kishin Najeriya.

Maganar zaman lafiya da hadin kai

Tinubu ya ce Sarkin Musulmin ya wuce matsayin mai sarauta, domin ya kasance jagora na gari, mai hada kan mabiya addinai daban-daban da kuma mai ba shugabannin kasa shawara.

Ya yaba da rawar da yake takawa a matsayin shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), da kuma shugaba tare da wani a majalisar hadin kan addinai ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai babban dalili: Makiyaya sun faɗi musabbabin shirin goyon bayan Tinubu

A cewarsa, karkashin jagorancinsa, Musulmi da Kiristoci sun samu damar fahimtar juna, inda bambancin addinai ya zama hanyar karfafa hadin kai maimakon haddasa rarrabuwar kai.

Tinubu ya kuma yaba da kokarin Sarkin Musulmin wajen samar da zaman lafiya a Arewa da yankin Sahel, bunkasa ilimi musamman na ’ya’ya mata, tallafa wa manoma da inganta kiwon lafiyar jama’a.

Mai alfarma Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi na yi wa jama'a bayani. Hoto: JNI
Source: Facebook

Tinubu ya yi wa sultan addu’a

Shugaban kasar ya bayyana cewa yana matukar daraja alakar abokantaka da ke tsakaninsa da Sarkin Musulmi, yana mai cewa shawarwarinsa sun kasance na gaskiya da kishin kasa.

Ya gode masa kan goyon baya da addu’o’in da yake yi wa Najeriya, tare da rokon Allah Ya ci gaba da ba shi lafiya, tsawon rai da karin hikima.

Tinubu ya yi addu’ar cewa mulkin Sarkin Musulmin ya ci gaba da kawo zaman lafiya a Sakkwato, hadin kai a Najeriya da daukaka ga al’ummar Musulmi.

Bago, Pantami sun taya Sultan murna

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya sake taso Bola Tinubu a gaba, ya fadi shirmen da ya yi

Bago ya bayyana Sarkin Musulmin a matsayin shugaba mai tawali’u, hakuri da tausayi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada addinin Musulunci da ci gaban al’umma.

Shi ma Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya taya Sarkin Musulmin murna, inda ya yaba da gudummawar da yake bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng