Nasara Babba: Sojoji Sun Kashe Shugabannin ISWAP da Mayaka Larabawa a Borno

Nasara Babba: Sojoji Sun Kashe Shugabannin ISWAP da Mayaka Larabawa a Borno

  • Sojojin Najeriya sun kashe Abu Hajara da Abul Walid, da wasu mayaƙan Larabawa biyu, yayin wani artabu da ISWAP a Kukawa
  • Rundunar ta ce ta kwato makamai da alburusai da dama, tare da na’urorin sadarwa bayan fafatawar da ta gudana ranar 31 ga Oktoba, 2026
  • Harin ya zo ne kwanaki uku bayan kashe ’yan ta’adda 55 a Buni Yadi, ciki har da wasu manyan kwamandojin ISWAP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe manyan shugabannin ƙungiyar ISWAP guda huɗu, ciki har da Larabawa biyu da wani babban kwamanda, tare da wasu mayakan ƙungiyar a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce an kashe ’yan ta’addan ne a ranar 31 ga Oktoba, 2026, yayin wani samame da dakarun haɗin gwiwa na Joint Task Force suka kai bayan da ISWAP ta kai musu babban hari a sansaninsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna da suka farmaki dakarun sojoji a Plateau

Sojoji sun kashe shugabannin ISWAP
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamban 2026.

Ya ce sojojin sun yi amfani da dakarun ƙasa da jiragen yaƙi na rundunar sama wajen tunkarar mayakan.

An kashe Abu Hajara da Abul Walid

A cikin sanarwar, Goni ya ce dakarun sun yi wa shugabanci da ƙarfin yaƙi na ISWAP babban lahani, bayan kashe wasu mayakanta yayin artabu a Kukawa.

Ya bayyana cewa daga cikin manyan ’yan ta’addan huɗun da aka kashe akwai Abu Hajara, wanda yake cikin fitattun mambobin majalisar shawarar ƙungiyar ta ISWAP.

Sauran sun haɗa da Abul Walid, wani babban kwamandan ƙungiyar kuma na kusa da Ba Shuwa, wanda shi ne babban Wali na ISWAP, da kuma wasu fitattun mayaƙan Larabawa biyu.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya gano hanyar da Tinubu zai samu kuri'u cikin sauki a 2027

Goni ya ce bayan artabun, sojojin sun kwato makamai da dama, alburusai da kuma na’urorin sadarwa daga hannun ’yan ta’addan.

Ya bayyana nasarar a matsayin shaida ta shirin ko-ta-kwana, ƙwarewa da ƙarfin makaman dakarun Operation Hadin Kai wajen ci gaba da matsa wa ’yan ta’adda lamba a yankin.

An kashe ’yan ta’adda 55 a Buni Yadi

Mohammed Goni ya ce harin da aka kai wa sansanin sojojin da ke Kukawa ya faru ne kwanaki uku kacal bayan wani farmaki a Buni Yadi, inda aka kashe ’yan ta’adda 55.

Daga cikin manyan kwamandojin da aka kashe a harin Buni Yadi akwai Ali Mandara Abba Gajiri, wanda aka fi sani da Munzir, da Habu Ikkima Nakif Yana Faruk, da kuma Kwamanda Gogore.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Operation Hadin Kai ke ci gaba da gudanar da hare-hare domin rage ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Sojoji sun kashe 'yan ISWAP a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda 217 tare da kama mutum 333 da ake zargi da ta’addanci a sassan Najeriya.

Dakarun sojojin sun kuma kuɓutar da mutane 349 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan a watan Oktoba na shekarar 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng