Dakarun Sojojin Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan ISWAP, an Kashe Manyan Kwamandoji da Mayaka

Dakarun Sojojin Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan ISWAP, an Kashe Manyan Kwamandoji da Mayaka

  • Rundunar sojojin saman Najeriya ta kashe ’yan ta’addar ISWAP 15 a wani samame da ta kai kusa da Kerenoa, a Ƙaramar Hukumar Marte ta Jihar Borno
  • Manyan kwamandojin ISWAP biyu, Abu Musanna da Hassan Abu Huraira, na cikin waɗanda aka kashe yayin harin
  • Sojojin sun lalata wani gini da ake zargin ana amfani da shi wajen adana kayan ƙera bama-bamai, yayin da gwamnan ISWAP na yankin ya samu munanan raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe ’yan ta’addar Boko Haram/ISWAP guda 15, ciki har da manyan kwamandojin ƙungiyar biyu, a wani samamen sama da ta kai a Jihar Borno.

Sojojin sun kuma lalata wani wurin da ake zargin ’yan ta’addar ke amfani da shi wajen adana kayan ƙera bama-bamai, a Ƙaramar Hukumar Marte ta jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Borno, sun kashe kusan 50

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Rundunar ta ce an gudanar da aikin ne da misalin ƙarfe 9:20 na daren ranar 28 ga Oktoban 2026, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ’yan ta’adda a yankin Kerenoa, da ke arewacin ƙaramar hukumar.

Yadda sojoji suka kai harin sama

Babban Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, mai gudanar da Operation Hadin Kai, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mukaddashin jami’in hulɗa da manema labarai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Laraba, 28 ga watan Oktoban 2026 a Maiduguri.

Sanarwar ta ce aikin ya ƙunshi sintirin bincike da kai hare-haren sama ta amfani da jiragen yaƙi, a matsayin wani ɓangare na ci gaba da kai hare-haren da aka tsara bisa bayanan sirri.

A cewar Goni, bayanan sirri sun nuna cewa ’yan ta’adda na gudanar da wasu ayyuka a kusa da Kerenoa, lamarin da ya sa rundunar ta tura jiragen yaƙi domin sa ido kan yankin.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, INEC ta amince da takarar Sheikh Pantami da Aminu Gwarzo a zaɓen 2027

Ya ce yayin aikin, sojojin saman sun gano wasu ’yan ta’adda biyu da ke kan babur, waɗanda suka nufi wani gini na wucin gadi da ke ƙarƙashin bishiya.

Bayan ci gaba da sa ido, sun gano wasu motsi a wajen ginin, wanda ya nuna cewa akwai ƙarin mayakan ’yan ta’adda a wurin. Daga nan ne jiragen yaƙin suka kai musu hare-hare masu tsauri.

An kashe Kwamandojin ISWAP 2

Rundunar sojin ta ce bayan tantance illar harin, an tabbatar da kashe ’yan ta’adda 15, yayin da aka lalata gine-ginen da ke wurin.

Ta ƙara da cewa an ga wata gobara ta tashi bayan harin, lamarin da ya nuna yiwuwar ana amfani da ginin da aka kai wa hari a matsayin wurin ajiyar kayan aikin ƙera bama-bamai na IED.

Sanarwar ta tabbatar da cewa manyan kwamandojin ISWAP guda biyu, Abu Musanna da Hassan Abu Huraira, na cikin waɗanda aka kashe a harin.

Haka kuma, wasu mayakan ƙungiyar da dama sun samu munanan raunuka, ciki har da Wali, wato gwamnan ISWAP na yankin, wanda rahoton rundunar ya ce ya ji rauni mai tsanani.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta kai wani hari na musamman da ta kai ta sama kan mayakan kungiyar ISWAP.

Rundunar sojojin ta ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ISWAP a yankin Tafkin Chadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng