Sarkin Musulmi Ya ba Peter Igho Sarauta a Daular Usmaniyya, An Sanya Lokacin Nadi
- Sarkin Musulmi zai nada Chief Peter Igho a matsayin Kakakin Daular Usmaniyya a wani bikin da za a gudanar a fadarsa da ke Sokoto
- An ba Igho sarautar ne tun ranar 10 ga Satumba, 2025, saboda gudummawar da ya bayar ga majalisar masarautar, Jihar Sokoto da Najeriya
- Igho ya shahara wajen shirya shirin talabijin, tare da horar da tsararrun kwararru a fannin yada labarai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, zai gudanar da bikin nada fitaccen mai watsa shirye-shiryen rediyo da talabijin, Chief Peter Igho, a matsayin Kakakin Daular Usmaniyya.
Sarkin Musulmin zai yi nadin ne ga Peter Igho a ranar Lahadi, 1 ga Nuwamban shekarar 2026.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce wata sanarwa daga fadar Sarkin Musulmi da ke Sokoto ta bayyana cewa za a gudanar da bikin a fadar, bayan an ba Igho sarautar tun ranar 10 ga Satumba, 2025.
An ba shi sarautar ne saboda gudummawar da ya bayar wajen bunkasa Majalisar Masarautar Sakkwato, Jihar Sakkwato da kuma Najeriya baki daya.
Za a samu manyan baki a wajen bikin
Ana sa ran bikin zai samu halartar fitattun ’yan Najeriya daga sassa daban-daban na kasar.
Manufar taron ita ce karfafa kyakkyawar alaka tsakanin al’ummomi tare da inganta hadin kan kasa, musamman a tsakanin al’ummomin Najeriya masu bambancin al’adu.
Sarkin Musulmi ne zai jagoranci bikin, inda zai karbi bakuncin mahalarta a fadarsa da ke Sokoto.
Peter Igho ya shahara a harkar talabijin
Chief Peter Igho fitaccen dan jarida ne, mai shirya fina-finan talabijin kuma kwararre a harkar yada labarai. Ya taba rike mukamin Daraktan Zartarwa a Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA).
Ya shahara musamman wajen shirya da jagorantar shirin wasan kwaikwayo na talabijin wanda yana daga cikin shirye-shiryen talabijin na farko da suka yi tasiri a Najeriya.
Baya ga wannan shiri, Igho ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da wasu shirye-shirye da suka taimaka wajen tsara yadda masana’antar watsa shirye-shirye ta Najeriya take a yau.
Ya samu lambobin yabo da dama na kasa da kasa saboda gudummawar da ya bayar a fannin watsa shirye-shirye. Haka kuma, ya horar da matasa da dama wadanda suka zama kwararru a harkar yada labarai.
Igho, wanda ya fito daga yankin Neja Delta, ya kuma yi fice wajen kare al’adu, jagorancin al’umma da ayyukan taimakon jama’a.
Sarkin Musulmi da rawar da yake takawa
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, shi ne mutum na 20 da ya hau gadon sarautar Daular Usmaniyya. Ya kuma kasance shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).
Ya hau karagar sarautar ne a ranar 2 ga Nuwamba, 2006. Kafin zama Sarkin Musulmi, ya yi ritaya daga aikin soja a matsayin Birgediya Janar a rundunar sojin Najeriya.

Source: Facebook
Sakon Sarkin Musulmi ga matasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya aika da sakon gargaɗi matasan Najeriya.
Sarkin Musulmin ya gargadi matasan Najeriya da kada su bari a yi amfani da su wajen aikata ayyukan ’yan daba saboda neman ribar siyasa ko ta kuɗi.
Asali: Legit.ng

