An Yi Babban Rashi: Shugaban FUT Minna na Farko kuma Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Babban Rashi: Shugaban FUT Minna na Farko kuma Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Farfesa Jonathan Ndagi, shugaban farko na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, babban birnin jihar Neja (FUT Minna), ya rasu
  • Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sanar da rasuwarsa tare da jinjina wa gudummawar da ya bayar a fannin ilimi
  • Marigayin ya kasance dattijo kuma masani wanda gudummawarsa ta sa aka ba shi sarautar gargajiya ta Wazirin Makaranta Nupe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, babban birnin jihar (FUT Minna) na farko bayan kafa ta, kuma Wazirin Makaranta, Farfesa Jonathan Ndagi, ya rasu.

Rahotanni sun bayyana dattijon wanda ake girmamawa saboda hidimar da ya yi wa al'ummaz ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 94 a duniya.

Jonathan Ndagi.
Tsohon shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, (FUT Minna) kuma Wazirin Makaranta, Farfesa Jonathan Ndagi Hoto: Abdullahi Bala Isa
Source: Facebook

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ne ya sanar da rasuwar fitaccen masanin ilimin, kamar yadda jaridar Leadership ta kawo.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da rasuwar babban dan kasuwa a Kano

Gwamnan Bago ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon shugaban jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna (FUT Minna), Farfesa Jonathan Ndagi.

A cikin saƙon ta’aziyyarsa, gwamnan ya amince da irin gagarumar gudummawar da marigayin ya bayar wajen bunƙasa ilimi da haɓaka ƙwarewar al’umma.

Ya bayyana shi a matsayin fitaccen masani kuma dattijo wanda tasirinsa ya zarce iyakokin Jihar Neja.

Ya lura cewa irin gudummawar da Farfesa Ndagi ya bayar ta sa aka karrama shi da sarautar gargajiya ta Wazirin Makaranta Nupe.

Gwamna Bago ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai basira, tawali’u, fara’a, tsoron Ubangiji da kuma tsayawa kan ƙa’idoji, inda ya ce tarihinsa ba zai gushe ba a tarihin FUT Minna da rayuwar dubban mutanen da ya shafa.

Bago ya miƙa ta’aziyyarsa

Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga Etsun Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar; mahukunta da ma’aikatan FUT Minna; da kuma iyalan marigayin na kusa da na nesa. Ya bayyana rasuwar tasa a matsayin babban rashi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara biyan tallafin N50,000 duk wata ga 'yan Najeriya, an ji masu amfana

A cewarsa, marigayin ya bar babban gurbi da zai yi wuya a samu wanda zai cike shi, idan aka yi la’akari da irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Neja da al’ummarta.

Karin bayani na tafe ..

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262