Lokaci Ya Yi: Babban Malamin Addinin Musulunci a Najeriya Ya Rasu a Jihar Zamfara

Lokaci Ya Yi: Babban Malamin Addinin Musulunci a Najeriya Ya Rasu a Jihar Zamfara

  • Jam’iyyar ADC reshen Jihar Zamfara ta yi alhinin rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Abubakar Aliyu Fari
  • Shugaban jam’iyyar a jihar, Hon. Kabiru Garba Gusau, ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi da jihar baki ɗaya
  • Ya roƙi Allah SWT Ya gafarta wa marigayin, Ya ba shi Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Babban malamin addinin Musulunci a Najeriya wanda ke zaune a jihar Sakkwato, Sheikh Abubakar Aliyu Fari ya riga mu gidan gaskiya.

An tabbatar da cewa malamin ya rasu ne a daren ranar Alhamis da ta gabata bayan fama da rashin lafiya.

Sheikh Abubakar Aliyu Fari.
Babban malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, Sheikh Abubakar Aliyu Fari Hoto: Munir Muhd
Source: Facebook

Jam'iyyar ADC ta yi ta'aziyya

Leadership ta ruwaito vewa jam’iyyar ADC reshen Jihar Zamfara ta tabbatar da haka a sakon alhini da ta fitar kan rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Abubakar Aliyu Fari.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun farmaki dan majalisar tarayya na APC a Kano da duwatsu

Shugaban jam’iyyar na jihar, Hon. Kabiru Garba Gusau, Ubandawakin Tudun Wada, ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi da jihar Zamfara baki ɗaya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin saƙon ta’aziyya da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar ADC na jihar Zamfara, Abdulkarim Umar Lihidda, ya sanya wa hannu ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, 2026 a Gusau.

Kabiru Garba ya jajanta wa iyalan marigayin, ’yan uwansa, ɗalibansa da mabiyansa bisa wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.

Ya roƙi Allah SWT Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya ba shi Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalansa ƙarfin zuciyar jure wannan rashi.

Kungiyar Izala ta yi alhini

Kungiyar Izala mai hedkwata a Jos reshen jihar Zamfara ta mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar malamin, tare da rokon Allah Ya gafarta masa.

ADC .
Tutar jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Twitter

Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Zamfara, Sheikh Abdullahi Umar Dalla Dalla, ya miƙa saƙon ta’aziyya bisa rasuwar babban malami Sheikh Abubakar Aliyu Fari.

Kara karanta wannan

Sarkin Katsina ya fita daban, ya faɗa wa tawagar Tinubu gaskiya ido da ido

Malamin ya ce:

"Wannan rashi babban rashi ne ga al’ummar Musulmi, musamman ɗalibai da malamai waɗanda suka amfana da iliminsa da gudummawar da ya bayar wajen yaɗa addinin Musulunci.
"Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa.
"Allah Ya ba iyalansa, ɗalibansa, abokan aikinsa da daukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi."

Limamin Juma'a a Gombe ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa babban limamin Masallacin Juma’a na Shagon Goro da ke jihar Gombe, Sheikh Sa'idu Imam ya riga mi gidan gaskiya.

Bayanai sun nuna cewa babban limamin, wanda malami ne a kungiyar Izala reshen jihar Gombe ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Tsohon ministan sadarwa kuma dan takarar gwamnan Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami ya tabbatar da rasuwar malamin, inda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan Sheokh Saidu Imam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262