Sojoji Sun Gano Wasu Bama Bamai da 'Yan Ta'adda Suka Dasa a Zamfara
- Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun gano tare da lalata bama-bamai da 'yan ta'adda suka dasa a hanyar Magami-Hannutara-Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara
- Bayan samun sahihan bayanan sirri, sojojin sun binciki yankin tare da gano wurare biyu da aka dasa abubuwan fashewar, inda suka lalata daya, suka kuma kwance dayan cikin aminci
- Rundunar ta kara tsaurara sintiri yayin Laftanar Janar Waidi Shuaibu ya gana da Gwamna Abdullahi Sule bayan kaddamar da karin sojoji a Nasarawa domin yaki da 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara – Dakarun Operation Fansan Yamma sun gano tare da lalata bama-bamai da 'yan ta'adda suka dasa a kan hanyar Magami-Hannutara-Dansadau, da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Dakarun sun dauki matakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan abubuwan fashewar da aka dasa domin haddasa babbar barna ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da lamarin ne a wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.
Yadda aka gano bama-baman
Bayan samun bayanan sirrin, sojojin sun tabbatar da tsaron yankin da abin ya shafa kafin gudanar da bincike mai zurfi.
Binciken ya kai ga gano wurare biyu da aka dasa abubuwan fashewar. Daga nan ne aka tura tawagar kwararru kan lalata bama-bamai da sauran abubuwan fashewa domin magance barazanar.
Tawagar ta lalata bam daya, sannan ta kwato dayan cikin aminci tare da kwance shi, ta yadda ba zai iya fashewa ba.
Rundunar ta ce dakarunta sun kara tsaurara sintiri da sa ido a yankin domin kare mazauna da masu amfani da hanyar, tare da hana sake aukuwar barazanar tsaro.
Ta kuma yi kira ga jama'a da su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa a muhallansu, tare da gaggauta sanar da hukumar tsaro mafi kusa idan suka ga wani abu ko motsi da suke zargi.
Rundunar ta jaddada muhimmancin kai rahoton abubuwan da ake zargin suna da hadari, domin bai wa jami'an tsaro damar daukar matakin da ya dace.
An tura karin sojoji Nasarawa
A wani bangaren kuma, Laftanar Janar Shaibu ya ce rundunar sojin Najeriya ta fadada daga rukunin sojoji guda takwas zuwa 12, matakin da ya ce yana bukatar karin karfin aiki, inganta yadda ake tura sojoji da kuma karfafa hadin gwiwa da hukumomin tsaro.
Ya ce kasancewar Nasarawa na dauke da wasu rundunonin sojoji da cibiyoyi, ciki har da makarantar horar da sojoji ta musamman da ke Doma, na iya taimakawa wajen fadada ayyukan tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya.
A cewarsa, karin kasancewar sojoji a yankin zai taimaka wajen saurin mayar da martani ga sabbin barazanar tsaro da kuma tallafa wa zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Martanin gwamna Abdullahi Sule
A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Sule ya gode wa hafsan sojin bisa zabar jihar Nasarawa a matsayin wurin kafa sababbin rundunonin sojoji.
Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ci gaba da zai inganta tsaro tare da samar da yanayin da ya dace domin bunkasar harkokin tattalin arziki da zamantakewa.
Ya tabbatar wa rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba su hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da kuma ba su damar sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu.
An kashe basarake a Kano
A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, dagacin kauyen Aujarawa da ke karamar hukumar Gezawa a jihar Kano, daga gidansa da sanyin safiyar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026.
Rahotanni sun ce maharan sun isa gidan da misalin karfe 1:30 na dare, suna tafiya a kafa tare da harbe-harbe a sama kafin su kutsa cikin gidan.
Sun harbi kofar shiga gidan, suka daure wasu daga cikin iyalansa da ke barci, sannan suka fitar da dagacin daga dakinsa suka tafi da shi suka kashe shi daga baya.
Asali: Legit.ng


